Tuna Baya: Lokacin da Aka Yi Yunkurin Kifar da Gwamnatin Obasanjo a Mulkin Farar Hula

Tuna Baya: Lokacin da Aka Yi Yunkurin Kifar da Gwamnatin Obasanjo a Mulkin Farar Hula

  • Ana ci gaba da rade-radin yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar juyin mulki
  • A shekarar 2004, an taba yunkurin kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, amma hakan bai yi nasara ba
  • An cafke wasu jami'an sojoji da ake zargin akwai hannunsu a yunkurin shirya kifar da gwamnatin Obasanjo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - A watan Afrilu 2004, Najeriya ta hana yunkurin juyin mulki da wasu jami’an soji suka kitsa don kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Wannan lamari ya jarraba sabuwar dimokuradiyyar kasar, bayan shekara biyar da dawo da mulkin farar hula.

An yi yunkurin yi wa Obasanjo juyin mulki a 2004
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce kusan jami’an sojoji guda 30 masu matsakaicin mukami 30 ne abin ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi yunkurin kifar da gwamnatin Obasanjo

Mai magana da yawun shugaban kasa a wancan lokaci, Remi Oyo, ta bayyana cewa an samu kutse ta fannin tsaro, wanda hakan ya sa aka gudanar da bincike har aka kama wasu da ake zargi.

Kara karanta wannan

Ana binciken tsohon gwamna kan zargin hannu a shirin yi wa Tinubu juyin mulki

"Shugaba Olusegun Obasanjo yana da cikakken amincewa da hukumomin tsaro da jami’an gwamnati."
"Ya yi amanna da al’ummar Najeriya, kuma ya san cewa ’yan Najeriya suna son dimokuradiyya, za su ci gaba da aiki da ita da kuma kare ta. Don haka abin da hukumomin leken asiri ke yi ba sabon abu ba ne, aikin su ne.”

- Remi Oyo

An gurfanar da sojoji kan yunkurin juyin mulki

Jaridar The New Humanitarian ta ce a watan Oktoba na shekarar 2004, an gurfanar da jami’an sojoji hudu da farar hula daya bisa zargin kulla makircin kashe Obasanjo ta hanyar harba makamin roka a kan jirginsa.

Jami’an da aka kama sun hada da Hamza Al-Mustapha, tsohon babban dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Laftanal Kanal Mohammed Umar Adeka, Yakubu Kudambo da Laftanal Tijani Abdallah, Laftanar. Farar hular kuwa shi ne Onwuchekwa Okorie.

An tuhume su da laifuffuka biyu na cin amanar kasa. Al-Mustapha, Adeka da Okorie sun musanta zargin a kotun tarayya da ke Legas, yayin da Kudambo da Abdallah aka gurfanar da su ba tare da halartarsu ba.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

Obasanjo ya sha kan yunkurin juyin mulki a 2024
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Zargin kulla makirci da neman roka

A cewar takardar tuhuma, Al-Mustapha ya bai wa Abdallah wasu kudade ta hannun Okorie tsakanin watan Nuwamba 2002 zuwa Maris 2004 domin sayen makamin roka mai linzami da za a harbi jirgin shugaban kasa da shi.

An kuma ce Abdallah ya yi wasu tafiye-tafiye zuwa Togo da Ivory Coast domin neman wannan makami na kasar Amurka.

Haka kuma, Kudambo ya rubuta takardar jawabin juyin mulki da aka tanada za a karanta bayan kifar da gwamnatin Obasanjo.

Batun zargin juyin mulki a 2025

A watan da ya gabata, gwamnatin tarayya ta soke shagulgulan faretin bikin cikar kasar shekara 65 da samun ’yancin kai a ranar 1 ga Oktoba.

Rahotanni sun ce soke faretin yana da nasaba da wani zargin yunkurin juyin mulki.

Sai dai hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta karyata wannan batu, inda ta ce soke faretin ba shi da alaka da kowane yunkurin juyin mulki da ake rade-radi a kansa.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin juyin mulki har Tinubu ya soke bikin ranar 'yanci? An samu bayanai

Kalu ya 'karyata' Obasanjo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi magana kan batun tazarcen Olusegun Obasanjo karo na uku.

Sanata Kalu ya zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da yin ƙarya kan ikirarin cewa bai nemi wa’adi na uku ba a mulkinsa.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya kira shi zuwa fadar shugaban kasa, inda ya tsagunta masa batun neman wa'adi na uku a kan mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng