Yadda Yan Sanda Suka Dakume 'Yan Jaridan Faransa 2 a Zanga Zangar Nnamdi Kanu
- ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan jarida biyu da ke daukar zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow a Abuja
- An kwace wayoyi da na'urar daukar bidiyo daga hannun ‘yan jaridar yayin da suka jami'an tsaron suka yi awon gaba da suka
- Shi ma lauyan Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor, ya shiga hannun ‘yan sanda a yayin da zanga-zangar ke gudana
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama wasu ‘yan jarida biyu na Agence France-Presse (AFP) a ranar Litinin.
An kama su ne yayin da suke daukar bidiyo na zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa ‘yan jaridar da aka kama sun hada da Nick Roll, dan asalin Amurka, da kuma John Okunyomih, dan Najeriya kuma mai daukar bidiyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An damƙe masu zanga-zanga a Abuja
Daily Post ta wallafa cewa an kama yan jaridan a kofar otal din Transcorp da ke Maitama lokacin da ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zanga.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun kutsa wajen daukar bidiyon yan jaridan tare da lalata kyamararsu.
Haka kuma, an kwace duka wayoyinsu, tare da cire kayan kariya daga hayakin barkono da suke sanye da su.
Amma an saki Nick Roll a wajen, amma an garzaya da Okunyomih zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar ‘yan sanda da ke Abuja, inda daga bisani aka sako shi.
'Yan sanda sun kama lauyan Nnamdi Kanu
Baya ga ‘yan jarida, jami’an ‘yan sanda sun kuma kama lauyan nan, Aloy Ejimakor, daya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar Nnamdi Kanu.

Source: Facebook
Tun da fari dai, an ga jami’an tsaro na harba barkonon tsohuwa a unguwar Central Business District a Abuja, inda masu zanga-zangar suka fara taruwa.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka wullawa hayakin ba masu anga-zanga ba ne, illa dai ma’aikata da suka tsaya jiran motoci zuwa wuraren aiki.
Zanga-zangar dai na karkashin jagorancin Omoyele Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters.
Nnamdi Kanu na tsare tun watan Yuni 2021 bayan an sake cafke shi, kuma har yanzu yana fuskantar shari’a a kotun tarayya da ke Abuja.
Sowore ya tsere bayan harbin yan sanda
A baya, kun ji cewa masu zanga-zangar neman a sake Nnamdi Kanu sun ruga da gudu bayan jami’an tsaro sun bude wuta da harsasai a babban birnin tarayya Abuja.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya jagoranci gangamin a wasu sassa na birnin tarayya Abuja kafin a tarwatsa shi da harbi da barkonon tsohuwa.
Jami’an ‘yan sanda, DSS, NSCDC da sojojin fadar shugaban ƙasa sun tsaurara tsaro a wurare masu mahimmanci a Abuja, musamman hanyar Fadar Shugaban Ƙasa a wannan rana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


