Yadda Gwamna Abba Ya Sa Baki a Rikicin Dan Jarida da Hadiminsa a Kano
- Dan jarida a Kano, Ibrahim Ishaq Rano ya bayyana rawar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taka a rikicinsa da Abdullahi Rogo
- Daya daga cikin manyan hadiman Gwamna, Abdullahi Rogo ya kai karar Ibrahim Ishaq ga yan sanda kan zargin bata suna
- Ɗan’uwan ya bayyana farin cikinsa tare da godiya ga gwamnan da sauran abokan aikin jarida da suka tsaya masa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fitaccen ɗan jarida a Kano, Ibrahim Ishaq Rano, ya bayyana godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.
Ya gode wa gwamnan bisa rawar gani da ya taka wajen warware matsalar da ta shiga tsakaninsa da wasu jami'in gwamnatin Kano, Abdullahi Rogo.

Source: Facebook
A cikin saƙonsa mai taken “Wasa Farin Girki” da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Danuwa Rano ya bayyana cewa gwamnan ya nuna kulawa da adalci.

Kara karanta wannan
Hadimin gwamnan Kano ya janye korafi a kan dan jarida, yan sanda sun saki Dan Uwa Rano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kano ya shiga batun dan jarida da Hadiminsa
Ibrahim Ishaq Rano ya ce Gwamnan Kano ya tura wakilci karkashin Babban Darakta na Musamman a gidan gwamnati, Manjo Janar Mohammed Sani mai ritaya domin sasanta lamarin.
Ya ce wakilan gwamnati sun kai ziyara har ofishin ‘yan sanda da ke shiyya ta daya, inda suka ba shi hakuri, tare da janye ƙorafinsu, tare da neman afuwa bisa abin da ya faru.
Rano ya bayyana cewa wannan mataki da Gwamna Abba ya ɗauka ya tabbatar da irin halin uba da jagora nagari da yake da shi.

Source: Facebook
Ya ce:
"Godiya ta ta musamman ga Mai girma gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf bisa shiga wannan magana da kuma saƙon wakilci da ya turo har Zone One ƙarƙashin jagorancin DG Special Services na gidan gwamnati, Major General Mohammed Sani (Rtd), suka karramani, suka janye ƙorafinsu tare da bani haƙuri kan wannan abu da ya faru."

Kara karanta wannan
Zargin bata sunan hadimin Gwamna Abba: 'Yan sanda sun yi magana kan tsare dan jarida
"Tabbas gwamna ka cancanta zama Uba ga ƴaƴanka. Allah Ya ƙara maka ƙwarin gwiwa domin cigaba da yin adalchi a tsakanin al'ummar da kake shugabanta."
Rano ya gode wa yan jarida da ‘yan sanda
Ibrahim Ishaq Rano ya miƙa godiya ga abokan aikinsa na jarida da suka nuna masa goyon baya da ƙauna a lokacin da ake fuskantar wannan rikici.
Ya ambaci fitattun mawallafa kamar Abdullatif Abubakar Jos na Solacebase, Jafar Jafar na Daily Nigerian da Buhari Abba na Kano Times.
Ya kafa da mika godiyarsa va Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo na Independent Post, da kuma Yakubu Musa Fagge na Lumana Radio International.
Danuwa Rano ya bayyana cewa irin wannan haɗin kai ya tabbatar masa da cewa akwai masoya na gaskiya a aikin jarida, kuma sun yi masa rana
Haka kuma, Rano ya jinjinawa lauyoyin da suka tsaya masa, musamman Barrister Umar Ɗanbaito da Barist Abba Hikima, saboda rawar da suka taka wajen kare haƙƙinsa.
Ya ƙara da yabawa rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyya ta daya da ke Kano bisa irin kyakkyawar mu’amala da suka nuna masa daga lokacin da aka gayyace shi har zuwa lokacin da aka sake shi.
Yan sandan Kano sun saki Danuwa Rano
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta saki ɗan jaridar Ibrahim Ishaq Rano, wanda aka fi sani da Dan’uwa Rano, da yammacin ranar Lahadi
An saki Dan jaridan ne bayan hadimin gwamnan jihar, Abdullahi Rogo, ya janye ƙorafin da ya kai a kansa na zargin bata suna ta cikin shirinsa da ya ke wallafa wa a intanet.
Kungiyar Amnesty International ta yi tir da kama Danuwa Rano, inda ta bayyana cewa irin wannan mataki “ya sabawa doka” da kuma haƙƙin faɗar albarkacin baki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
