'Yan Ta'adda Sun Hallaka Kwamandan Bataliyar Sojojin Najeriya da Wasu Jami'ai
- Mayakan Boko Haram sun kai hari Borno, inda suka kashe kwamandan bataliyar soji ta 202, sojoji biyar da ’yan CJTF uku
- An ce 'yan ta'addar sun yi wa sojojin Najeriya kwanton bauna a hanyarsu ta komawa gari bayan kakkabe sansanonin miyagu
- Rundunar Operation Hadin Kai ta bayyana cewa sun kashe da dama daga ’yan ta’addan, kuma suna bibiyar hanyoyin sadarwarsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno – Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai mummunan harin kwanton bauna kan dakarun sojojin Najeriya.
'Yan ta'addar sun kashe kwamandan bataliyar soji ta 202 da wasu sojoji biyar da 'yan C-JTF uku a harin da ya faru a kauyen Kashimiri, karamar hukumar Bama, jihar Borno.

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun yi wa sojoji kwanton bauna

Kara karanta wannan
Zargin bata sunan hadimin Gwamna Abba: 'Yan sanda sun yi magana kan tsare dan jarida
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wasu sojoji da dama sun jikkata, ciki har da kwamandan bataliya ta 222 da ke Konduga, yayin da aka yi garkuwa da wani soja daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne yayin da dakarun suke dawowa daga wani aikin kakkabe sansanonin ‘yan ta’adda da suka gudanar a ranar Juma’a, inda aka yi musu kwanton bauna a kan hanyarsu ta komawa Bama.
Wani soja da ya tsira daga harin ya bayyana cewa abin ya faru ne a kauyen Kashimiri, kimanin kilomita 25 daga garin Bama da kilomita 93 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Sojan ya ce:
“An tura mu aikin kakkabe maboyar ‘yan ta’adda bayan rahotanni na leƙen asiri sun nuna cewa wasu kungiyoyin Boko Haram daga wurare daban-daban sun hadu domin kai hari a Bama, Kawuri ko Awulari.
"Aikinmu a rundunar sojoji ta 7 shi ne mu tarwatsa shirinsu. Mun cika umarni — mun lalata sansaninsu, mun ceto mata da yara, amma ba mu san sun shirya mana kwanton bauna ba.”
'Yan ta'adda sun kashe kwamandan sojoji
Sojan ya ci gaba cewa:
“Mun rasa kwamandan bataliya ta 202, sojoji biyar da mambobin JTF uku nan take. Sun bude mana wuta daga baya, da muka juya mu kare kanmu, wani rukuni ya harba mana RPG daga gaba. Harsasai suka rika sauka kanmu ta ko’ina.
"Kwamandan da sojojin da ke kusa da shi suka mutu nan take. Wani harin RPG ya tarwatsa wani dan JTF, inda ya mutu a wurin.
"Abin na ci mana rai idan mutane suna cewa an kashe mu a fafatawa, don mun kammala aikinmu lafiya, amma aka yi mana kwanton bauna a hanyar dawowa Bama. Wannan shi ne gaskiyar yaki.”
Sojan ya kuma bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kashe 'yan ta'adda da dama yayin aikin share sansanoninsu, inda wasu daga cikinsu suka tsere da munanan raunukan harbi.

Source: Original
Borno: Nasarar sojoji kan 'yan ta'adda
Sojan ya ce abin takaici ne yadda babu wanda ke magana kan irin nasarorin da suka samu, ciki har da kisan 'yan ta'addar da lalata sansanoninsu, inji rahoton SaharaReporters.
Ya bayyana nasarorin da suka samu kan 'yan ta'addar da cewa:
"Har yanzu ana tattara gawarwakin ‘yan ta’addan da muka halaka, amma babu wanda ke magana a kai. A matsayarmu na jami’an tsaro, mun saba da sadaukar da rayukanmu don kare kasarmu.

Kara karanta wannan
Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su
"Mun kwashe gawarwakin mutum takwas, sojoji biyar da JTF uku, amma mun kama rediyon miyagun suna tattaunawa, inda muka ji suna kiran sunan wani sojanmu mai suna Bello da suka kama da ransa.
"Suna amfani da tashar Channel 8 wajen sadarwa, kuma muna ci gaba da bibiyar saƙonninsu. Idan suna kirga sunayen mayakansu, idan wani bai amsa ba, sai su ce ‘ya yi barci’, ma’ana ya mutu.”
Wani babban jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce sojojin ba su karaya ba, suna nan da kwarin gwiwarsu.
An kashe kwamandan sojoji a Borno
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa, Boko Haram ta kai hari wani sansanin soji na Borno, inda suka kashe kwamandan soji da wasu jami'ai.
'Yan ta'addan sun kai harin ne da motocin yaki, inda suka kona gine-gine da motoci, tare da jikkata sojoji, sannan aka yi zargin sun sace wasu jami'an.
Wannan harin ya biyo bayan wani farmaki a Damboa, inda 'yan ta'addar Boko Haram suka kashe sojoji da dama, yayin da aka nemi wasu aka rasa bayan harin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
