Zargin Batan Sunan Hadimin Gwamna Abba: 'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Tsare Dan Jarida

Zargin Batan Sunan Hadimin Gwamna Abba: 'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Tsare Dan Jarida

  • Jami'an rundunar 'yan sanda sun cafke wani dan jarida bisa zargin bata sunan hadimin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • 'Yan sandan sun cafke dan jaridan ne lokacin da yake aiki a ofishinsa, inda suka tsare shi a hannunsu don yi masa tambayoyi
  • Rudunar 'yan sandan ta tabbatar da cewa za ta gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci kan zargin da ake yi masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama tare da tsare wani ɗan jarida da ke Kano, Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano.

Rundunar 'yan sandan ta tsare shi ne bayan wani korafi da aka ce babban hadimin gwamnan Kano kan al’amuran fadar gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar a kansa.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Sojojin sama sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Neja

'Yan sanda sun cafke dan jarida a Kano
Sufeto Janar na 'yan sanda tare da Ibrahim Ishaq Danuwa Rano. Hoto: Nigeria Police Force, Yunus Maulud
Source: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa an kama Dan’uwa Rano ne a ranar Asabar a ofishinsa da ke cikin birnin Kano.

'Yan sanda sun cafke dan jarida a Kano

Shaidu sun ce jami’an ‘yan sanda daga hedkwatar shiyya ta daya suka kama shi ba tare da gabatar da takardar iznin cafke shi ba.

An kama ɗan jaridar ne bisa zargin ɓata suna, da kuma wani shirin barkwanci mai suna Imalu da ake watsawa a tasharsa ta YouTube – Dan’uwa TV.

A cikin shirin, an yi ishara da wani “daraktan al’amuran fadar gwamnati” da ake zargin yana karɓar rashawa don bai wa baƙi damar yin ganawa da gwamna.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram, ISWAP sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Duk da cewa ba a ambaci suna kai tsaye ba, Abdullahi Ibrahim Rogo ya shigar da korafi yana cewa shirin ya yi nufin tozarta shi.

Dan’uwa Rano ya tabbatar cewa ana yi masa tambayoyi ne kan shirin da kuma zargin gudanar da tashar talabijin ta yanar gizo ba tare da lasisi ba.

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta shiyya ta daya, CSP Bashir Muhammad, ya tabbatar da kama ɗan jaridar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.

“AIG Ahmed Garba ya umarci a gayyaci ɗan jaridar don bincike. Bayan cikakken bincike, idan an same shi da laifi, za a gurfanar da shi a kotu.”

- CSP Bashir Muhammad

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

'Yan sanda sun kama dan jarida a Kano
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ta shiyya ta daya za ta bi doka da gaskiya wajen gudanar da binciken, kuma za ta tabbatar da cewa an gudanar da shi cikin adalci tare da bayyanawa jama’a sakamakon abin da suka samu.

Sai dai, Rogo, wanda ake zargin shi ne ya shigar da ƙorafin, yana fuskantar bincike daga hukumar EFCC da ICPC bisa zargin almundahanar Naira biliyan 6.5, wanda ake zargin ya aikata ta hannun wasu wakilai tsakanin Nuwamba 2023 zuwa Fabrairu 2025.

Gwamnatin Kano ta maka Ganduje a kotu

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Bago ya samo hanyar magance 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta shigar da kara kan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa.

Gwamnatin ta gurfanar da Ganduje, 'ya'yansa biyu da wasu mutane a gaban babbar kotun jihar bisa zargin almundanar N4.4bn.

Ana zargin an karkatar da fiye da N4.49bn da aka ware domin gina hanyoyi, samar da wutar lantarki da katanga domin amfanin kamfanoni masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng