Wata Sabuwa: An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC Mai Mulki
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta dauki matakin ladabtarwa kan daya daga cikin mutanen da ke jan ragamar shugabancinta a jihar Edo
- An dakatar da shugaban jam'iyyar APC a wata mazaba da ke karamar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo
- Jam'iyyar APC ta bayanin dalilin dakatar da shugaban wanda ta bada umarnin a hana shi halartar duk wasu tarurruka da suka dangance ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Jam’iyyar APC mai mulki ta dakatar da daya daga cikin shugabanninta a jihar Edo.
Jam'iyyar APC ta dakatar da Mallam Adamu Ototobor, wanda shi ne shugaban mazaba ta 9 a karamar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo, daga duk wata harkar jam’iyyar har sai an samu wani sabon umarni.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce dakatarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar APC na jihar Edo, Prince Peter Uwadiae, wadda ya fitar a ranar Asabar, 18 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa APC ta dakatar da shugabanta a Edo?
Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa shugaban na APC za ta fara aiki ne nan take.
A cewar sanarwar, an dakatar da Ototobor ne bayan binciken halayensa da ayyukansa na baya-bayan nan, wadanda jam’iyyar ta ce ba su daidaita da tsarin ladabi, biyayya da dokokin jam’iyyar a jihar Edo.
“An umurci shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Etsako ta Gabas da ya hana Mallam Adamu Ototobor halartar ko shiga cikin kowane taro, zama ko wani taron jam’iyya har sai lokacin da aka dage dakatarwarsa a hukumance.”
- Prince Peter Uwadiae
Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa ladabi, biyayya da girmama hukumomi sune ginshikin APC, kuma duk wani aiki da zai iya lalata waɗannan kimomi ba za a lamunta da shi ba.

Source: Original
Karanta wasu karin labaran kan jam'iyyar APC
- Zaben gwamna: APC na da ‘yan takara 14 da ke son karɓar mulki daga PDP a Osun
- Yadda gwamnatin APC ta jawo yunwa da matsalar tsaro a Najeriya, ADC ta fasa kwai
- Yaron Jonathan da ya taba zama 'dan majalisa ya watsar da PDP zuwa APC
- Diri: Jam'iyyar APC ta fara zawarcin gwamnan da ya fice daga PDP, ta bayyana dalili
- Ba tare da boye boye ba, PDP ta fadi dalilin da ya sa gwamnoninta komawa APC
- NNPP ta wanke Tinubu daga zargin tursasawa 'yan adawa sauya sheka zuwa APC
Uba Sani ya ce APC za ta samu kuri'u
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi magana kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa jam'iyyat APC za ta samu kuri'u kaso 95% cikin 100% a jihar Kaduna a zaben shekarar 2027.
Ya bada tabbacin cewa babu sauran wata adawa a jihar Kaduna domin duk mafi yawancinsu sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

