'Yar Ƙwaya ce fa Yanzu': Sanata Ya Ƙaryata Zargin Cin Zarafin Matarsa a Gidan Aure

'Yar Ƙwaya ce fa Yanzu': Sanata Ya Ƙaryata Zargin Cin Zarafin Matarsa a Gidan Aure

  • Sanata daga jihar Delta a Najeriya, Ned Nwoko ya yi magana kan jita-jitar yana cin zarafin matarsa a gidan aure
  • Sanatan ya yi martanin ne bayan wani bidiyo ya nuna matarsa Regina Daniels cikin tashin hankali da aka danganta da aurensu
  • Ya ce Regina ta lalata kadarori da dukan ma’aikata saboda shaye-shaye, inda ya bayyana cewa tana bukatar jinya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sanata Ned Nwoko ya mayar da martani bayan bidiyon da ake yadawa kan cin zarafin matarsa.

Sanatan ya yi jawabi bayan wani faifan bidiyo da ya nuna matarsa, jaruma Regina Daniels, tana cikin tashin hankali ya yadu a yanar gizo.

Sanata ya yi martani kan rigima da matarsa
Sanata Ned Mwoko da matarsa, Regina Daniels. Hoto: @regina.daniels.
Source: Instagram

Sanata ya magantu kan matarsa, Regina Daniels

A cikin sakonsa da ya wallafa a Facebook, Nwoko ya ƙaryata labarin da ake yadawa musamman a kafofin sadarwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

An nemi tayar da gobara a matatar Dangote da wasu matsaloli sama da 20

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matsalar da ke tsakaninsu ta samo asali ne daga shaye-shaye da jarumar ke yi, musamman miyagun kwayoyi da giya.

Ya bayyana cewa:

"Regina ba ta kasance haka ba tun da farko, amma yanzu shaye-shaye ne ke lalata rayuwarta da dangantakarmu.”

Abubuwan da Regina Daniels ke yi

Sanatan ya kara da cewa Regina ta tayar da hankali a gidansa, ta doki ma’aikata uku da kuma lalata motoci da tagogin gida ba tare da dalili ba.

Ya ce ya ba ta zabin jinya a Asokoro ko Jordan domin ta ci gaba da karbar maganin ta, inda ba za ta iya samun kwayoyi ba.

Nwoko ya kuma zargi abokanta da haddasa rikicin, yana cewa wasu daga cikinsu suna kawo mata miyagun kwayoyi.

Ya ce a lokacin da yake asibiti da ɗansu Moon, an tayar da tarzoma a gida da Sammy, wanda ya kira babban mai kawo mata kwayoyi.

Sanata Nwoko ya magantu kan halin da Regina Daniels ke ciki
Sanata Ned Nwoko da matarsa jaruma, Regina Daniels. Hoto: Senator Prince Ned Nwoko.
Source: Instagram

Daniels: Martanin kanin matar Sanata Ned Nwoko

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero abubuwan da suka jawo karyewar farashin abinci warwas

Sai dai kanin jarumar, Sammy West, ya mayar da martani yana zargin Nwoko da dukan Regina, tare da alwashin kare ’yar uwarsa.

Ya rubuta cewa:

“Inda namiji ke dukan mace, ko da ba ’yar uwata ba ce, zan tsaya in yi fada da jinina.”

Meye Regina Daniels ta ce kan haka?

Har yanzu babu amsar martani daga Regina ko wakilanta game da zargin da Nwoko ya yi wanda ya jawo maganganu a shafukan sadarwa a kasar.

Regina Daniels da Ned Nwoko sun yi aure tun 2019, auren da ya ja hankalin jama’a saboda bambancin shekaru mai yawa a tsakaninsu.

Regina Daniels ta tada kura a kafar sadarwa

A baya, kun ji cewa shahararriyar jarumar Nollywood Regina Daniels ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da bidiyonta da biloniyan mijita Ned Nwoko a wajen wani biki ya bayyana.

Masoya sun garzaya shafin jarumar inda suka dunga jinjina mata kan daukakar da ta samu wanda ya sha banban da na yan fim a Najeriya.

Ma'auratan sun dauki hankali a wajen bikin da aka yi a Abuja wanda yake na diyar takwaran mijinta ne, Sanata Sani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.