An Yi Yunkurin Juyin Mulki Har Tinubu Ya Soke Bikin Ranar ’Yanci? An Samu Bayanai

An Yi Yunkurin Juyin Mulki Har Tinubu Ya Soke Bikin Ranar ’Yanci? An Samu Bayanai

  • Sojojin Najeriya sun yi karin haske ka yada cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya
  • Rundunar ta kuma yi magana kan cewa har an kama wasu jami'an sojoji 16 da ake zarginsu da hannu a juyin mulki
  • Hedikwatar Tsaron Ƙasa ta bayyana cewa labarin da ya danganta soke bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai da juyin mulki ba gaskiya ba ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hedikwatar Tsaron Ƙasa (DHQ) ta yi martani kan rade-radin da ake yadawa wai an yi yunkurin juyin mulki a Najeriya.

Rundunar ta karyata jita-jitar da wasu kafafen labarai suka yada cewa soke bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai ya samo asali ne daga yunkurin juyin mulki.

Rundunar tsaro ta musanta rahoton yunkurin juyin mulki a Najeriya.
Hafsan tsaron Najeriya da Malam Nuhu Ribadu. Hoto: HQ Nigerian Army, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar, Birgediya-janar Tukur Gusau ya sanyawa hannu wanda aka wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Minista ya tafi kasar waje, ya je duba jiragen yakin sojojin Najeriya da ake kerawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jita da ake yadawa kan juyin mulki

Wasu rahotanni sun yi ta yada cewa gwamnatin Bola Tinubu ta soke bikin ranar 'yancin kai ne na cikar Najeriya shekaru 65 saboda fargabar juyin mulki.

A rahotannin da ake yadawa har da jaridar Sahara Reporters, an ce an kama wasu manyan sojoji har 16 da ake zargin suna da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu.

Wannan ba shi ne karon farko da ake yada irin wannan jita-jita, a baya ma an sha kiran sojoji da su yi gaggawar kifar da gwamnatin Tinubu saboda halin kunci da ake ciki.

Rundunar tsaro ta musanta yunkurin juyin mulki a Najeriya
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa yayin taro a Abuja. HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Meye sojoji suka ce kan rahoton juyin mulki?

Rundunar ta bayyana cewa wannan labari ƙarya ne tsagwaro wanda aka shirya don ta da hankalin jama’a da ɓata sunan sojojin ƙasa.

A cewar sanarwar, an soke bikin ne saboda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci wani muhimmin taron haɗin gwiwa a ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Zaben 2019: Yadda Akpabio ya yi karyar an yi masa magudin zabe a gaban Sanatoci

Sannan hakan zai ba dakarun soji mayar da hankali wajen yaƙar ta’addanci, ‘yan bindiga da masu tayar da zaune tsaye a ƙasar.

Ta kuma bayyana cewa binciken da ake yi kan jami’an sojoji 16 lamari ne na cikin gida don tabbatar da tsaro da biyayya a cikin runduna.

Sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa suna nan daram kan biyayya ga tsarin mulki da gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da ƙarya da masu yada jita-jita.

Kiran juyin mulki: Gwamnatin Tinubu ta yi gargadi

A baya, mun ba ku bayani cewa Fadar shugaban kasa ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen da ake yi a Najeriya kan neman a yi juyin mulki.

Fadar ta yi wannan magana ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce abin takaici ne yadda ake mantawa da alherin gwamnatin Bola Tinubu.

Hakan ya biyo bayan wani rahoto da wata jarida ta buga kan halin kunci da ake ciki da bai yiwa gwamnatin dadi ba wanda har wasu ke kiran a yi juyin mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.