Malaman Musulunci Sun Magantu kan Zargin Kisan Kiristoci, Sun Roki Tunibu

Malaman Musulunci Sun Magantu kan Zargin Kisan Kiristoci, Sun Roki Tunibu

  • Malaman addinin Musulunci daga yankin cin Najeriya sun gudanar da babban taro na musamman a jihar Kaduna
  • A zamansu, malaman sun karyata zargin da wasu ‘yan siyasa na kasashen waje ke yi na “kisan gillar Kiristoci” a Najeriya
  • Sun bukaci gwamnati ta shawarci CAN ta fito fili ta nesanta kanta daga zargin, domin irin wadannan kalamai na raba kawuna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Malaman addinin Musulunci da shugabanni daga sassan Arewacin Najeriya sun yi zama a jihar Kaduna.

Malaman Musulunci sun musanta zargin da ake yadawa na cewa ana kisan gillar Kiristoci a Najeriya.

Malaman Musulunci sun soki zargin kisan Kiristoci
Gamayyar malaman Musulunci yayin taro a Kaduna. Hoto: JIBWIS Nigeria.
Source: Facebook

Malaman sun fadi hakan ne bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Kaduna wanda JIBWIS Nigeria ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin kisan kiyashin Kiristoci a Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya tara malaman Musulunci a Zamfara, ya nemi alfarmarsu

A baya dai dan majalisar Amurka, Sanata Ted Cruz, ya gabatar da kudirin kariya ga Kiristoci a Najeriya saboda abin da ya kira kisan kiyashi da cin zarafin addini.

Amma gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi, inda Majalisar Dokoki ta kasa ta yanke shawarar yin mu’amala kai tsaye da majalisar Amurka don wanke kasar daga wannan batu.

Har ila yau, mutane daidaiku da kungiyoyi sun yi Allah wadai da zargin inda suka ce hakan zai kawo fitina a cikin al'umma bayan fama da rashin tsaro da ake yi.

Kisan Kiristoci: Gargadin Malaman Musulunci

Yayin taron, malaman Musulunci sun ce irin wannan ikirari na raba kawunan ‘yan kasa da zai kara kawo matsala a tsakanin al'umma.

Malaman sun bukaci gwamnatin tarayya da ta shawarci kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da ta fito fili ta karyata wannan zargi domin hana yada labaran karya.

Malaman Musulunci sun gana a Kaduna
Shugaban Izalah, Sheikh Bala Lau yayin taron malaman Musulunci a Kaduna. Hoto: JIBWIS Nigeria.
Source: Facebook

Rokon malaman Musulunci ga gwamnatin tarayya

Sun kuma roki kafafen yada labarai da kasashen waje da su rika bayar da rahotanni na gaskiya da za su karfafa hadin kai da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Cikin wata sanarwa da suka fitar, malaman sun yi kira ga gwamnati ta dauki matakai na kawo sulhu da tsaro musamman a yankunan da rikici ya daɗe yana addabar su.

Sun ce sulhu ba wai kawai ya tsaya ga tattaunawar manya ko hare-haren soja ba, dole ya kunshi gyara da sake gina al’umma.

Malaman sun kuma nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu, inda suka la’anci harin Isra’ila a Gaza da cewa keta hakkin dan Adam ne.

Sannan suka yaba wa gwamnatin Najeriya bisa matsayinta na goyon bayan Falasɗinu a Majalisar Dinkin Duniya, tare da kira ga musulmai su ci gaba da addu’a da tallafi.

CAN ta bukaci Tinubu ya kawo karshen kashe-kashe

Mun ba ku labarin cewa kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa al'ummomin Kirista.

CAN ta nuna cewa ta dade tana ankarar da kasashen duniya ta'addancin da ke ritsawa da mabiya addinin Kirista.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.