Saudi Ta Rage Adadin Kujerun Najeriya bayan Fara Shirin Rage Kudin Hajjin 2026

Saudi Ta Rage Adadin Kujerun Najeriya bayan Fara Shirin Rage Kudin Hajjin 2026

  • Najeriya za ta samu kujeru 66,910 kacal a aikin Hajjin 2026 bayan Saudiyya ta rage adadin da aka saba ba ta
  • Hukumar aikin hajji ta kasa, NAHCON ta bayyana dalilin da ya sa kasa mai tsarki daukar matakin a 2026
  • An sanar da sauyin ne a taron da hukumar ta yi da jihohi don tattauna batun rage kudin Hajji da aka ce a yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, AbujaSaudiyya ta rage adadin kujerun aikin Hajji da take bai wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 a shekarar 2026.

Sabon tsarin na nufin cewa Najeriya za ta rasa fiye da kujeru 28,000 daga abin da ta saba samu a shekarun baya.

Shugaban hukumar NAHCON
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman. Hoto: Jibwis Nigeria|Inside Haramain
Source: Facebook

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana dalilin rage guraben a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara binciken yadda $35m da aka ware don gina matatar mai ta yi layar zana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'ar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta ce sabon tsarin zai shafi yadda za a sake rabon kujeru tsakanin jihohi bisa la’akari da yadda suka yi amfani da kujerunsu a bara.

Saudi ta rage kujerun Hajjin Najeriya

NAHCON ta bayyana cewa adadin kujerun da Saudiyya ta ware wa Najeriya a 2026 ya tsaya ne kan 66,910 kacal.

Hakan na nufin cewa duk da cewa Najeriya ta samu damar samun mahajjata 95,000 a 2024 da 2025, ba za ta iya tura fiye da 66,910 ba a shekarar 2026.

An dauki matakin ne sakamakon rashin cika adadin mahajjatan da aka ware wa kasar a shekarun 2024 da 2025.

Shugaban NAHCON ya kira da a hada kai

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bukaci shugabannin jihohi da su hada kai domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2026.

Mahajjatan Najeriya a 2025
Mahajjatan Najeriya yayin tafiya aikin Hajjin 2025. Hoto: National Hajj Commission
Source: Facebook

Ya jaddada muhimmancin tantance lafiyar mahajjata kafin tafiya, yana mai cewa Saudiyya tana matukar damuwa da batun lafiya.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman banza: Gwamnatin Tinubu ta bude cibiyoyin samar da aiki a jihohi

Yadda za a raba kujerun Hajji

Kwamishinan ayyukan NAHCON, Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa rarraba guraben zai dogara ne da yadda kowace jiha ta cika kujerunta a 2025.

Daily Trust ta rahoto cewa ya ce jihohin da suka yi amfani da kujerunsu yadda ya kamata za su samu fifiko a rabon 2026.

Kokarin rage kudin Hajjin 2026

A yayin taron, NAHCON ta sanar da cewa tana kokarin tattaunawa da masu hidima domin rage kudin da ke da alaka da jigilar kaya da sauran ayyuka.

An kuma bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya duba yiwuwar rage 2% na kudin da ake karba daga mahajjata.

Wakilin bankin CBN a NAHCON, Adetona Sikiru Adedeji, ya ce zai isar da bukatar NAHCON ga Babban Bankin domin ganin an rage wannan kudi don saukaka wa masu niyyar aikin Hajji.

NAHCON ta yaba wa Tinubu, Shettima

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yaba wa shugaba Bola Tinubu kan rage kudin Hajji.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Haka zalika ya yaba wa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima kan rawar da ya taka wajen neman rage kudin.

NAHCON ya fitar da sanarwar ne bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umarni da a sake duba kudin Hajjin 2026 domin rage shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng