Gwamnatin Tarayya Ta Soke Amfani da JAMB wajen Shiga Jami’a? An Samu Bayanai
- Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske kan jita-jitar da ke yawo cewa JAMB ba zai sake zama wajibi wajen samun gurbin shiga jami’o’i ba
- A yau gwamnatin ta musanta soke JAMB din wanda ya zama dole kafin samun gurbin shiga makarantun gaba da sakandire a Najeriya
- Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya bayyana cewa JAMB ne kadai hukumar da doka ta ba izinin gudanar da jarrabawar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana gaskiya kan labaran da ke yawo a wasu kafafen yada labarai na soke jarabawar JAMB.
Gwamnatin ta musanta labarin soke jarabawar a Najeriya domin samun gurbin shiga jami'o'i da makarantun gaba da sakandare.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta wallafa a Facebook a ranar Alhamis da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Boriowo Folasade.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da gaske an soke jarabawar JAMB a Najeriya?
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa labarin da ke yawo “ba shi da tushe kuma ƙarya ce da aka ƙirƙira.”
Ya ce Ma’aikatar ba ta taɓa fitar da wata sanarwa ko bayar da izinin cewa an cire JAMB daga tsarin karɓar ɗalibai ba.
A cewarsa:
“Domin kawar da shakku, JAMB ita ce kadai hukumar da doka ta amince da ita don gudanar da jarrabawar shiga jami’a da tsara tsarin karɓar ɗalibai a dukkan manyan makarantu a Najeriya.
"Tsarin karɓar ɗalibai ta hannun JAMB yana nan yadda yake, kuma duk wani labari da ya saba da haka ya kamata a yi watsi da shi.”

Source: Facebook
Alkawarin ministan ilimi ga yan Najeriya
Ministan ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da haɗin gwiwa da JAMB da sauran hukumomi domin tabbatar da gaskiya, adalci da cancanta a tsarin karɓar ɗalibai.
Ma’aikatar ta kuma yi kira ga ɗalibai, iyaye da jami’o’i da su dogara kawai da hanypyin sadarwa na hukuma daga Ma’aikatar Ilimi da JAMB don samun sahihin bayani.
Ta kuma yi gargadi ga kafafen yada labarai da shafukan yanar gizo, da su guji yada labaran da ba a tabbatar da su ba, tana mai cewa hakan na iya haifar da rudani a fannin ilimi.
“Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na sake jaddada cewa babu wani sauyi a matsayin JAMB, wacce ke da muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin karɓar ɗalibai a ƙasar nan."
- Cewar sanarwar
Ma’aikatar ilimi ta kuma shawarci jama’a da su rika ziyartar shafukan yanar gizo da na kafafen sada zumunta na hukuma na Ma’aikatar Ilimi da JAMB don samun bayanai masu inganci.
Gwamnati ta fadi makarantun kyauta a Najeriya
Kun ji cewa gwamnati ta sanar da cewa ɗaliban kwalejojin fasaha (FTC) za su ci gaba da karatu kyauta ba tare da biyan kudin makaranta ba.
Rahotanni sun bayyana cewa shirin ya haɗa da ɗaukar nauyin kayan makaranta, littattafai da wasu muhimman abubuwa.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya gargadi shugabannin makarantu da kada su karɓi kudin da ba a ba su izini ba daga wajen iyaye.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

