Katsina: An Tsinci Gawar Jami’in Kwastam bayan Kwana da Mata 3 a Otal

Katsina: An Tsinci Gawar Jami’in Kwastam bayan Kwana da Mata 3 a Otal

  • An gano gawar wani jami’in Kwastam, Lawal Tukur, a ɗakin otal a cikin garin Katsina bayan ya kwana tare da mata
  • An samu wasu magunguna ko sinadarai a ɗakin da aka same shi, yayin da aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti
  • Hukumar Kwastam ta tabbatar da samun rahoton lamarin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin musabbabin mutuwar jami’in

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Hukumar Kwastam ta tabbatar da samun rahoton tsintar gawar wani daga cikin jami'anta a cikin otal da ke Katsina.

An samu gawar jami’in hukumar Kwastam mai suna Lawal Tukur, wanda yake da mukamin mataikamin sufritanda (ASC).

Jami'in Kwastam ya mutu a otal din Katsina
Shugaban hukumar Kwastam, Bashir Adewale. Hoto: Nigeria Customs Service.
Source: Facebook

A ina aka samun gawar jami'in na Kwastam?

Rahoton Zagazaola Makama ta ce an gano gawarsa a ɗakin wani otal a cikin birnin Katsina da ke iyaka da kasar Nijar.

Kara karanta wannan

Atiku: "Gaskiya ta fito da ministan Tinubu ya tona asiri kan kwangilar Legas zuwa Kalaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 15 ga Oktobar 2025, a Murjani Hotel da ke tsakiyar birnin Katsina, inda jami’in ya sauka a matsayin bako.

Wasu rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan otal ɗin ne suka gano gawar Tukur da safe misalin ƙarfe 8:30 na safe, suka kuma sanar da shugabannin otal da jami’an tsaro.

Majiyoyi daga otal ɗin sun bayyana cewa an samu wasu sinadarai da ake zargin magunguna ne a cikin sharan ɗakin da mamacin ya kwana.

Ana bincike kan samun gawar jami'in Kwastam a otal din Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Mata nawa suka kwana da jami'in Kwastam?

An ce mata uku ne suka kasance a otal ɗin a lokacin da lamarin ya faru daga cikinsu akwai Khadija Ali mai shekaru 34 daga unguwar Dutsin Amare, Katsina.

Sai kuma Aisha Lawal mai shekaru 30 daga karamar hukumar Ingawa da Hafsat Yusuf da ke da shekaru 22 daga unguwar Brigade da ke Kano, cewar rahoton Tribune.

Rahotanni sun nuna cewa Khadija da Aisha ne suka kwana tare da jami’in, yayin da Hafsat ta ziyarce su daga baya ta kuma zauna a otal ɗin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama miji da mata masu safarar makamai ga ƴan ta'adda a jihohin Arewa

Bayan an samu labarin rasuwa ma'aikacin, an kai gawarsa zuwa Asibitin Gwamantin Tarayya (FMC) da ke Katsina.

Daga nan ne kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa, sannan aka kai gawar zuwa ɗakin ajiye gawa domin ci gaba da bincike.

Hukumar Kwastam ta tabbatar da samun labarin lamarin, tana kuma haɗa kai da jami’an tsaro domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar jami’in hukumar.

An samu gawar shugaban NDLEA a otal

A baya, mun ba ku labarin cewa an shiga fargaba bayan samun gawar shugaban hukumar NDLEA reshen jihar Cross River a dakin otal wanda ya tayar da hankali matuka.

Majiyoyi sun ce an tsinci gawar Morrison Ogbonna a wani otal da ke birnin Calabar da ke jihar a ranar Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025 da ta gabata.

Abokan aikinsa da suka zo daukarsa sun ce sun buga ƙofa sau da yawa ba tare da amsa ba, daga bisani aka same shi matacce wanda ya tayar da hankulan al'ummar da ke yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.