Wale Edun: Ministan Kudi Ya Bayyana a London duk da Rahoton Rashin Lafiyarsa
- Ministan kudin Najeriya, Wale Edun, ya bayyana a taron baje kolin fasahar Afirka da aka gudanar a London
- Bidiyo ya nuna Edun yana jawabi ga bakin da suka halarci baje kolin a O’DA Art Gallery a Somerset House
- Hakan na zuwa ne bayan cewa ministan bai da lafiya da jita jitar cewa yana tafi ganin likita a kasar waje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
London – Ministan kudi, Wale Edun, ya bayyana a wani baje kolin fasaha a London bayan jita-jitar da ta yadu cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani.
An hangi ministan ne a rumfar O’DA Art Gallery yayin baje kolin da ake gudanarwa a Somerset House daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba.

Source: Getty Images
Legit ta tabbatar da hakan ne a wani bidiyo da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayyanar tasa ta kawo karshen rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ministan na fama da matsananciyar rashin lafiya.
An hango ministan kudi a London
Baje kolin fasahar Afirka na bana ya samu halartar ‘yan Najeriya da dama ciki har da O’DA Art Gallery, wacce ta nuna ayyukan fasaha na Simon Ojeaga, Paul Majek da Afeez Onakoya.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Wale Edun yana jawabi ga bakin da suka taru a wajen baje kolin, yana bayyana muhimmancin tallafa wa fasahar Afirka.
Bidiyon ya tabbatar da cewa ministan yana da lafiya, duk da jita-jitar da ta yadu a kwanakin baya game da tsananin rashin lafiya da ya ke fama da ita.
Fadar shugaban kasa ta ce Edun hutu ya je
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da cewa ministan na Birtaniya ne domin hutu.
A cewar Onanuga, Edun ya je hutun ne bayan gajiyar da ya sha wajen gudanar da al’amuran tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan
Daga karshe, an garzaya da ministan Tinubu ketare domin jinyar cutar da ke damunsa
“Ministan kudi Wale Edun ya ziyarci baje kolin zane a London. Yana birnin ne don hutu na ‘yan kwanaki bayan fama da wahalhalun aikin gyara tattalin arziki,”
Inji Onanuga
Edun bai je taron IMF Amurka ba
Kafin bayyanar Edun, wasu rahotanni sun yi nuni da cewa ministan ya kamu da rashin lafiya kuma zai tafi kasashen waje jinya.
A ranar Lahadi, Onanuga ya tabbatar cewa Edun ya dan sami rashin lafiya, abin da ya sa ba shi ne ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF a Amurka.
A maimakon haka, gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, ne ya jagoranci tawagar kasar zuwa taron.

Source: Twitter
Rahotanni daga Abuja sun ce ministan ya bar babban birnin kasar zuwa Legas da yammacin Litinin kafin ya tashi zuwa kasashen waje domin duba lafiyarsa.
IMF ta ce ana fitar da kudi daga Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa asusun ba da lamuni na duniya ya ce ana fitar da haramtattun kudi daga Najeriya zuwa ketare.
IMF ya yi alkawarin tallafawa Najeriya da wasu kasashen duniya wajen yaki da satar kudin gwamnati.
Shugabar IMF ce ta bayyana haka yayin taron da ake na shekara shekara a Amurka, inda gwamnan CBN ya wakilci Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

