Da Gaske Boko Haram Sun Ƙwace Iko da Barikin Sojoji a Borno? An Gano Gaskiya
- An yi ta yada wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna Boko Haram sun mamaye barikin sojoji na Najeriya
- Binciken kwa-kwaf ya gano gaskiya kan yada bidiyo da aka yi ta yadawa, inda aka gano ainihin inda abin da ya faru
- An ce sojoji a cikin bidiyon suna sanye da kayan da ke ɗauke da tutar Sudan, kuma motocin da suke ciki na dauke da rubutu a harshen Larabci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - An cika kafofin sada zumunta na zamani da wani faifan bidiyon yan Boko Haram a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta ya nuna wasu mutane cikin kayan sojoji suna murna da ihu da cewa sun yi nasara, inda aka ce Boko Haram ba ne a Najeriya.

Source: Twitter
An yada cewa Boko Haram sun kwace bariki
Wani mai amfani da X mai suna @K3lv1nB0b0 ne ya yada bidiyon, yana cewa Boko Haram sun kwace barikin sojojin Najeriya inda suke ta ihu da murna kan nasarar da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, an ga motocin da ke dauke da dakarun da makamai, suna harbe-harbe tare da murna da yi magana cikin harshen da ba a gane ba.
Bidiyon ya karade shafukan sada zumunta inda ya dauko hankulan jama'a da dama inda fiye da mutane miliyan daya da wasu dubbai suka yada da kuma yin tsokaci daban-daban.

Source: Facebook
Mene ne bincike ya gano game da bidiyon?
Sai dai binciken TheCable ya gano cewa wannan bidiyo ba daga Najeriya ba ne, kuma ba yan Boko Haram ba ne ke cikinsa.
An gano bidiyon tun farko an saka shi a shafukan sada daban-daban a watan Satumbar shekarar 2025 daga wani shafin kasar Sudan da ke da rubuce-rubucen Larabci.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
A cewar fassarar rubutun, an bayyana bidiyon da kalmomin “nasara daga Allah”, wanda ke nuna yana da alaka da rikicin Sudan.
Bidiyon ya bayyana motocin dakarun dauke da rubutu da harshen Larabci, tare da dakarun sanye da kayan da ke da tutar Sudan.
Sudan dai tana fama da yakin basasa tun watan Afrilun shekarar 2023 tsakanin sojojin gwamnati da kungiyar 'Rapid Support Forces' da ke neman iko.
A bisa wannan bincike, an tabbatar cewa bidiyon ba na Najeriya ba ne, don haka ikirarin cewa Boko Haram ne karya ne babu wata hujja da ke tabbatar da haka.
Sojoji sun illata 'yan Boko Haram a Borno
Mun ba ku labarin cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato makudan kudaden fansa da suka karba a hannun bayin Allah a yankuna da dama na jihar da ke Arewa maso Gabas.
Jami'an tsaron sun kuma raunata 'yan ta'adda a yayin artabun da aka dauki dogon lokaci ana gudanarwa wanda ya jawo ilata bangaren yan ta'addan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
