Asiri Ya Tonu a Amurka: IMF Ya Ce ana Fitar da Haramtattun Kudi daga Najeriya
- Asusun IMF ya nuna damuwa kan yadda fitar kudin haram daga Najeriya ke kara tabarbarewar tattalin arzikin kasar
- Shugabar IMF, Kristalina Georgieva, ta ce ana mayar da hankali kan bin diddigin kudin da ake sace wa daga Najeriya
- Georgieva ta ce za a karfafa horo da amfani da fasahar zamani wajen ganowa da daukar mataki kan kudin da ake zargi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Asusun ba da lamuni na IMF ya bayyana cewa fitar haramtattun kudi daga Najeriya na kara tsananta matsalar samun kudin shiga da kuma gina tattalin arzikin kasa.
Shugabar IMF, Kristalina Georgieva ce ta bayyana hakan a taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya da ke gudana a birnin Washington DC.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Georgieva ta ce za a mayar da hankali wajen bibiyar irin wadannan kudi domin rufe gibin da ke kawo asarar kudin gwamnati da lalata ci gaban kasa.

Kara karanta wannan
Dalilin majalisa na kafa kwamiti kan zargin yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IMF: Fitar kudi na barazana ga tattali
Georgieva ta bayyana cewa fitar haramtattun kudi ya zama barazana mai tsanani ga tsaron kudi da tattalin arzikin kasashe masu tasowa.
Ta ce irin kudin sun hada da satar dukiyar gwamnati da kuma mu’amalar kudi ta yanar gizo da ba a iya gano asalin su.
A cewarta, wadannan matsaloli suna rushe tsarin mulki, suna lalata kudin jama’a, tare da gurgunta ci gaban al’umma.
“Da fasahar zamani, za a iya boye kudin da aka sata cikin sirri, abin da ke wahalar da gano su,”
Inji ta
IMF ta karfafa yaki da sata a Najeriya
IMF ya bayyana cewa ya sabunta tsarin AML da CFT domin inganta bin diddigin kudin da ake sace wa a Najeriya da wasu kasashe.
Georgieva ta ce yanzu bin sawun kudin ya zama bangare na duba ingancin tattalin arziki na kowace kasa da ake yi a duk shekara.
Ta kara da cewa IMF yana hada bayanai daga abubuwan da suka gabata cikin tsarin tantance tsarin kudi domin gano gibin da ake samu wajen satar kudin gwamnati.
Haka kuma, kasashen da ke neman tallafin IMF za su fuskanci sharuɗɗa na musamman da za su shafi dakile irin wadannan matsaloli.

Source: Facebook
Duk da haka, IMF ya ce tattalin arzikin Najeriya ya karu da 3.9% a 2025 kuma ana hasashen zai karu da 4.2% a 2026.
IMF zai horas da kasashen duniya
Shugabar ta bayyana cewa IMF na ba kasashe taimako ta fuskar horaswa da kayan aiki na zamani domin taimaka musu wajen ganowa da kuma dakile safarar kudi.
Ta ce:
“Muna bukatar horas da hukumomin kasashe domin su kware wajen gano irin wadannan kudi, su bi diddiginsu cikin sauri, su kuma dauki mataki kafin su ɓace.”
Cardoso ya wakilici Najeriya a taron IMF
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa gwamnan CBN, Yemi Cardoso zai wakilci kasar a taron IMF.
Da farko dai, ministan kudi, Wale Edun ne aka tsara zai jagoranci tawagar amma ya gaza hakan saboda rashin lafiya.
An yi rade radin cewa Edun ya kamu da mummunar rashin lafiya, amma fadar shugaban kasa ta karyata labarin tana mai cewa yana samun sauki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
