Duniya Labari: Babban Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Duniya Labari: Babban Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga cocin Katolika da al’ummar Kirista bisa rasuwar babban malami
  • An tabbatar da rasuwar Fasto Michael Olatunji Fagun, tsohon malamin coci da ya ba da gudunmawa sosai da ya ke raye
  • Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin bawan Allah mai tsantseni wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa bishara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga cocin Katolika da al’ummar Kirista a Najeriya bayan rasuwar Fasto.

Shugaba Tinubu ya nuna alhinin ne bisa rasuwar Rabaran Michael Olatunji Fagun, tsohon babban malamin a jihar Ekiti.

Tinubu ya yi addu'o'i bayan samun labarin rasuwar Fasto
Marigayi Michael Fagun da Bola Tinubu. Hoto: Catholic Africa, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tinubu ya yi jimamin mutuwar Fasto Fagun

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mista Bayo Onanuga ya fitar wanda The Nation ta samu a ranar Talata 14 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Farouk Lawan: Tsohon 'dan majalisa ya rabu da Kwankwasiyya bayan barin kurkuku

Shugaban ƙasar ya bayyana marigayin a matsayin bawan Allah nagari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada bishara da taimakon ɗan adam.

Rabaran Fagun, wanda aka naɗa a watan Yuli 1965 daga bisani an ɗaukaka shi zuwa matsayin limami a watan Oktoba 1971.

Marigayin ya fara aiki a matsayin Rabaran mai taimakawa a tsohon babban coci na Ondo daga 1971 zuwa 1972, kafin Fafaroma Paul VI ya kafa majami'a na Ado-Ekiti.

Tinubu ya aike da sakon ta'aziyya bayan mutuwar Fasto
Shugaba Bola Tinubu yayin taron jami'an tsaro a Abuja. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Yabon da Bola Tinubu ya yi wa Faston

Shugaba Tinubu ya yaba wa marigayin bisa tsayin daka da hidima wajen yaɗa addinin Kirista, bunƙasa ilimi da cigaban al’umma, yana mai cewa marigayin ya rayu da tawali’u, sauƙi da tsantseni kamar yadda Almasihu ya koyar.

Ya ce:

“Rabaran Fagun ya rayu don fadada bishara a Najeriya da wasu sassan duniya, yana kai wa jama’a bishara har ƙauyuka, tare da haɗa koyarwar kalmar Ubangiji da ayyukan jinƙai.”

Ya kuma bayyana Rabaran Fagun a matsayin malami mai ilimi na harsuna da dama wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka mabiya Katolika da gina kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma, cewar Arise News.

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Wike da Tinubu? An ji gaskiyar abin da ya faru

Shugaban ƙasar ya yi ta’aziyya ga dangin Fagun, coci na Ekiti, da dukkan masu jimami, yana mai addu’ar Allah ya jikansa da rahama kuma ya ba iyalansa da mabiya haƙuri da kwanciyar hankali.

“Ayyukan alheri da gagarumin sadaukarwarsa za su ci gaba da kasancewa abin tunawa har abada.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya jajanta bayan mutuwar Fasto

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ta’aziyya bayan sanar da rasuwar babban malamin addinin Kirista a Najeriya a jiya ranar Talata 14 ga watan Oktoban 2025.

Tinubu ya yi jimamin mutuwar Fasto Uma Ukpai, wanda ya kafa kungiyar 'Uma Ukpai Evangelistic' da kuma ba da gudunmawa sosai lokacin da yake raye.

Ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin jajirtattu da suka ba da gudunmawa a bangaren bangaskiya wanda ya aiwatar da aikin da aka aiko shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.