An Ji Ta Bakin 'Yan Kasuwa kan Dalilin Tashin Farashin Man Fetur a Najeriya

An Ji Ta Bakin 'Yan Kasuwa kan Dalilin Tashin Farashin Man Fetur a Najeriya

  • Farashin litar man fetur ya karu zuwa kusan N1,000 a wasu birane sakamakon wasu matsalolin jigila da aka samu a fadin Najeriya
  • Kungiyar ‘yan kasuwar mai ta kasa (IPMAN) ta zargi masu rumbun ajiya da kara farashi bayan Dangote ya dakatar da lodin mai
  • ‘Yan kasuwa sun ce suna shirin fara shigo da man fetur daga kasashen ketare kai tsaye don dawo da gasa da rage farashi a kasuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Farashin litar man fetur a Najeriya ya kai kusan N1,000 yayin da ake ci gaba da fama da karancinsa da hauhawar farashi a gidajen mai.

Kungiyar dillalan man fetur (DAPPMAN) da ta ‘yan kasuwar mai ta kasa (IPMAN) za su fara shirin shigo da mai kai tsaye.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Gidan mai a Najeriya
Mutane na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa hakan na zuwa ne yayin da matatar Dangote ke fuskantar tsaiko a samar da mai, abin da ya haddasa karuwar farashi da dogayen layuka a gidajen mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan kasuwa na shirin shigo da man fetur

Mai magana da yawun IPMAN, Chinedu Ukadike, ya tabbatar da cewa wasu kamfanoni sun kammala shirye-shiryen shigo da man fetur daga kasashen waje.

Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen dawo da gasa a kasuwa, wanda zai sa farashin ya ragu idan farashin da suke kawowa ya fi na Dangote rahusa.

“Kasuwa gasa ce. Idan wasu sun kawo mai mai araha, tabbas sauran za su bi sawu kuma hakan zai rage farashi,”

- In ji Ukadike

Farashin ya tashi daga N865 zuwa N950 a cikin ‘yan kwanaki, inda wasu gidajen mai ke sayarwa tsakanin N920 da N955, yayin da wasu a Abuja, Lagos da Sokoto ke kai N1,000 a lita.

Kara karanta wannan

Shehi ya nemi zama da Kiristoci kan zuwan Isra'ila Najeriya da barazanar yaki

Dalilin tashin farashin man fetur

IPMAN ta daura alhakin hauhawar farashin a kan manyan diloli da suka kara farashin sayar da mai bayan Dangote ya dakatar da lodin mai na wasu kwanaki.

The Cable ta rahoto cewa shugaban IPMAN, Abubakar Shettima, ya ce:

“Dangote na dakatar da lodin mai, masu rumbun ajiya suka hanzarta kara farashin daga N830 zuwa kusan N890.”

Bincike ya nuna cewa Matrix, Fynefield da Liquid Bulk suna sayar da mai a N900, yayin da Pinnacle ke N885, RainOil N890, NIPCO N850, Aiteo N878, da Sigmund N890.

Matatar Dangote ta dakatar da lodin mai

Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote ta dakatar da lodin man fetur na dan lokaci, lamarin da ya kara matsa lamba kan isar da mai a kasar.

Wasu majiyoyi sun ce dakatarwar ba ta rasa nasaba da gyaran injuna ko rikicin cikin gida bayan sallamar wasu injiniyoyi da dama daga kamfanin.

Matatar Dangote a Legas
Wani sashe na matatar Dangote a Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Duk da kokarn samun karin bayani, Dangote bai fitar da wata sanarwa kai tsaye kan dalilin dakatarwar har yanzu.

Kara karanta wannan

Trump ya bar mata tsirara, tsarinsa ya jefa masu ciki a barazanar kanjamau

A baya, matatar ta sanar da tsarin rarraba mai kai tsaye ga gidajen mai da zai sa farashi ya sauka zuwa N841 da, amma hakan bai tabbata ba.

PENGASSAN: Kamfanin Dangote ya yi godiya

A wani rahoton, kun ji cewa an kammmala takun saka da aka yi tsakanin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN.

Rikicin da aka yi tsakanin Dangote da kungiyar ma'aikatan mai ta PENGASSAN ya haifar da yajin aiki a Najeriya.

Bayan gama rikicin, Dangote ya lissafa mutane da dama ya musu godiya saboda rawar da suka taka, ciki har da shugaba Bola Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng