Dangantaka Ta Yi Tsami tsakanin Wike da Tinubu? An Ji Gaskiyar Abin da Ya Faru
- An yada wasu rahotanni masu nuna cewa sabani ya shiga tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike da Shugaba Bola Tinubu
- Nyesom Wike ya fito ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da shugaban kasan
- Ministan ya bayyana cewa abin da aka yadawa ko kadan babu gaskiya a cikinsa, inda ya yi bayani kan dalilin rashin ganinsa wajen taron majalisar koli ta kasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa yana cikin sabani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wike ya bayyana cewa rashin halartarsa taron Majalisar koli ta kasa na makon jiya ya samo asali ne daga wasu muhimman ayyukan gwamnati da ya riga ya tsara zai gudanar.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Wike ya bayyana hakan ne yayin bude hanyoyin shiga unguwar Dakibiyu, Abuja, ranar Talata, 14 ga watan Oktoban 2025.
An yada labarin sabani tsakanin Tinubu da Wike
Rahotanni sun bayyana cewa Wike ya kaurace wa taron ne bayan Shugaba Tinubu ya ki amincewa da dan takarar da ya fi so domin zama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Shugaba Tinubu ya gabatar da sunan Farfesa Joash Amupitan ga majalisar don tabbatarwa, yayin da ake cewa Wike ya fi son a zabi mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman.
Me Wike ya ce kan sabani da Tinubu?
Wike ya bayyana cewa ya sanar da Shugaba Tinubu tun kafin taron cewa ba zai samu damar halarta ba, tare da ba da umarnin cewa karamar Ministar Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, ta wakilce shi, za a samu labarin a Leadership.

Kara karanta wannan
Daga karshe, an garzaya da ministan Tinubu ketare domin jinyar cutar da ke damunsa
“A makon jiya, ranar Alhamis, muna da wani taron kaddamar da aiki, kuma na gaya wa karamar Ministar Abuja ta wakilce ni a taron Majalisar koli ta kasa."
"Na riga na sanar da shugaban kasa cewa ba zan samu damar halarta ba saboda wasu ayyukan da muka riga muka tsara."
- Nyesom Wike
Meyasa Wike bai je taron majalisar koli ba?
Ya bayyana rahotannin da ke alakanta rashin halartarsa taron majalisar koli da fushi kan zaben shugaban INEC a matsayin farfaganda marar tushe da nufin bata suna, yana mai shawartar jama’a da su yi watsi da su.

Source: Twitter
“Shi ya sa dole mu rika taka-tsantsan da irin wadannan farfaganda da bata suna. Amma duk da haka, a ci gaba da maida hankali domin cimma nasara."
"Suna cewa ban halarci taron ba ne saboda ba a zabi mutumin da na fi so ba, wannan karya ce."
- Nyesom Wike
Gwamna ya umarci saka hular Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya ba mukarraban gwamnatinsa sabon umarni kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Okpepholo ya umarci mukarraban gwamnatinsa da su rika sanya hular Asiwaju a duk lokacin da za su halarci taron majalisar zartarwar jihar.
Monday Okpebholo ya ce ya dauki wannan matakin ne domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu a matsayinsa na mai kishin kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

