'Kotun Tarayya Ta Wanke Abba Kyari,' Lauya Ya Fito da Bayanai
- Lauyan Abba Kyari, Hamza Suleiman, ya ce kotu ta yi watsi da bukatar mika Kyari Amurka tun 2022 kuma ba a daukaka kara ba
- Ya bayyana cewa Abba Kyari bai taɓa karɓar ko kobo daga Hushpuppi ba, kuma babu wata alaka ta kuɗi tsakaninsu
- Hamza Suleiman ya yi bayani da cewa rikicin ya samo asali ne daga bambancin tsarin doka tsakanin Najeriya da Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Lauyan Abba Kyari, mai suna Hamza Suleiman, ya ce kotu ta wanke dan sandan daga zargin karɓar kuɗi daga dan damfara, Ramon Abbas, da aka fi sani da Hushpuppi.
Ya ce kotun ta yi watsi da bukatar mika Kyari zuwa Amurka tun ranar 29 ga watan Agusta, 2022, kuma har yanzu ba a daukaka kara ba.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa Suleiman ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya a Abuja, inda ya yi bayanin cewa hukuncin kotun yana aiki har yanzu.
An yi watsi da bukatar mika Kyari Amurka
A cewar Suleiman, dokar Najeriya ta tanadi cewa ba za a iya mika wani dan kasa zuwa wata kasa ba sai da izinin kotu.
Ya ce:
“Tun lokacin da kotu ta yi watsi da karar, babu wani mataki da aka kara dauka. Wannan hukunci yana nan daram bisa tsarin doka.”
Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa Kyari ya karɓi kuɗi daga Hushpuppi, yana mai cewa babu wani takamaiman hujja da ke nuna haka.
“Kyari bai karɓi kudin Hushpuppi ba,” Lauya
Lauyan ya bayyana cewa Abba Kyari bai taɓa karɓar ko kobo daga Hushpuppi ba, haka kuma ba a taɓa mayar masa da kuɗin da ‘yan sanda suka kashe wajen binciken da Hushpuppi ya kai ba.
Suleiman ya ce Hushpuppi ne ya kai ƙarar wani mutum da ya zarge shi da barazanar kashe mahaifiyarsa, amma daga baya aka gano cewa wanda ake zargi ɗan damfara ne irin shi.
Lauyan ya ce:
“An kama wanda ake zargi, amma saboda matsalolin lafiya aka ba shi beli bayan mako uku.
Wannan ya fusata Hushpuppi wanda ya so a tuhume shi da laifin fashi da makami, amma Kyari ya ƙi.”
Bambancin tsarin doka ya jawo rudani
Suleiman ya ce rikicin da ya biyo baya ya samo asali ne daga bambancin tsarin shari’a tsakanin Najeriya da Amurka.
A cewarsa,
“A Najeriya, ba laifi ba ne idan wanda ya kai ƙara ya taimaka da ɗan kuɗin man fetur ko masauki ga ‘yan sanda da ke bincike, musamman ganin yadda gwamnati ke da ƙarancin kuɗin bincike. Amma a Amurka hakan laifi ne.”
Ya ce wannan ne ya jawo wasu a kasashen waje suka ɗauka cewa Kyari ya yi laifi, alhali ba haka lamarin yake ba.
Akwai alakar kudi tsakanin Kyari da Hushpuppi?
Suleiman ya kara bayyana cewa sau biyu ne Kyari da Hushpuppi suka yi waya — a watan Janairu da Mayu na shekarar 2020.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
Ya ce sun yi magana ne domin batun kariya ga mahaifiyar Hushpuppi da kuma wani abokinsa Martins da aka zarga da zambar ₦8m.

Source: UGC
Ya ce:
“Kyari bai karɓi wani abu daga waɗannan al’amura ba, kuma babu wata alaka ta kasuwanci ko ta aikata laifi tsakaninsu.”
An nemi Tinubu ya saki Abba Kyari
A wani rahoton, mun kawo muku cewa an fara kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Abba Kyari Afuwa.
Tsohon ministan wasanni, Barista Solomon Dalung ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Kyari da ake tsare da shi.
An fara kiran ne bayan shugaban kasar ya yi wa wasu da aka kama da manyan laifuffuka afuwa, ciki har da Maryam Sanda da ta kashe mijinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

