Daga karshe, an Garzaya da Ministan Tinubu Ketare domin Jinyar Cutar da Ke Damunsa

Daga karshe, an Garzaya da Ministan Tinubu Ketare domin Jinyar Cutar da Ke Damunsa

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauki minista a gwamnatin Bola Tinubu zuwa Birtaniya domin duba lafiyarsa
  • Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun, ya tashi zuwa Birtaniya ne bayan ya kwanta rashin lafiya a kwanan nan
  • Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa bai samu bugun zuciya ba, amma ya keɓe yana jinya kuma yana samun kulawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa kan lafiyar minista a gwamnatin Bola Tinubu da ake ta magana a kai.

Fadar ta tabbatar da cewa ministan Kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin ƙasa, Mr. Wale Edun, ya tafi zuwa Birtaniya domin nema wa kansa magani.

An tabbatar da tafyar minista zuwa Birtaniya saboda rashin lafiya
Ministan kudi, Wale Edun tare da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Minista ya tafi Birtaniya neman lafiya

Rahoton Punch ya ce majiyoyi masu kusanci da gwamnati sun tabbatar haka a safiyar Talata 14 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko, majiyoyi farko sun bayyana cewa Edun, wanda ya kwanta rashin lafiya a kwanan nan, ya bar Abuja zuwa Lagos.

A daren Litinin ne ya bi jirgin fasinja zuwa Lagos daga nan kuma ya tashi zuwa London ta jirgin 'British Airways'.

Kafin tafiyarsa, wasu jami’an fadar shugaban ƙasa sun shaida cewa Edun yana jinya a gidansa da ke Abuja ƙarƙashin kulawar likitocin Najeriya.

Majiyoyi sun ce, duk da cewa rashin lafiyarsa ya ɗan yi tsanani, ba bugun zuciya ba ne kamar yadda ake rade-radi.

“Eh, gaskiya ne ba shi da lafiya. Amma ba bugun zuciya ba ne. A ranar Lahadi yana cikin gidansa. Amma likitoci sun ba da shawarar cewa ya je waje domin ƙarin kulawa,”

- Cewar wata majiya

Haka kuma, wani na kusa da ministan ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kulawa da lafiyar Edun sosai, duk da haka babu wani shiri na maye gurbinsa.

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Wike da Tinubu? An ji gaskiyar abin da ya faru

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan labarai da dabarun yada bayanai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da cewa ministan ya yi rashin lafiya yar ba zata amma yana samun sauƙi.

“Eh, Wale Edun yana rashin lafiya, amma yana murmurewa. Yana da shekara kusan 69 yanzu, kuma yana samun kulawa sosai."

- Bayo Onanuga

Fadar shugaban kasa ta musanta shirin sauya minista
Ministan kudi da inganta tattalin arziki, Wale Edun. Hoto: Federal Ministry of Finance.
Source: Getty Images

Gwamnati ta musanta shirin sauya Wale Edun

Fadar shugaban ƙasa ta kuma musanta jita-jitar cewa ana shirin sauke Edun daga mukaminsa, sai dai ta tabbatar cewa ba zai halarci taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF ba a Washington DC.

Tun bayan nadinsa a ranar 28 ga Agusta, 2023, Edun ya taka muhimmiyar rawa a gyaran tsarin tattalin arzikin gwamnati ta Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, da daidaita farashin canjin kuɗi.

Har zuwa lokacin wannan rahoton, ma’aikatar kudi ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da halin lafiyar ministan ko inda yake.

Jinya: Gwamnan CBN ya wakilci minista

Kun ji cewa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF.

Kara karanta wannan

Babban albishir da Kashim Shettima ya yi wa yan Najeriya kan halin kunci

Ministan kudi, Wale Edun, ba zai halarci taron ba saboda rashin lafiya, inda Cardoso zai maye gurbinsa a taron da za a yi a kasar Amurka.

Taron zai gudana daga ranar 13 zuwa 17, Oktoba, 2025, tare da tattaunawa kan ci gaban kasa, tattalin arziki, da kasuwannin kudi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.