‘Kowa Ya Bi’: Gwamna Ya Umarci Dukan Mukarrabansa kan Sanya Hular Tinubu

‘Kowa Ya Bi’: Gwamna Ya Umarci Dukan Mukarrabansa kan Sanya Hular Tinubu

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da samun goyon baya musamman daga gwamnonin Najeriya
  • Daya daga cikin gwamnoni a Najeriya ya umarci dukan mukarrabansa su rika sanya hular shugaban domin nuna goyon baya
  • Gwamna Monday Okpebhola na Edo gargade su cewa duk wanda bai sanya hular ba, ba zai shiga taron majalisar ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin City — Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ba da umarni ga dukan kwamishinoni da masu ba shi shawara kan goyon bayan Bola Tinubu.

Gwamnan ya umarce su, su rika sanya hular Asiwaju a duk lokacin da za su halarci taron majalisar zartarwa ta jihar.

Gwamna ya umarci mukarrabansa kan sanya hular Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo na Edo. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Umarnin Gwamna ga mukarrabansa kan hular Tinubu

The Nation ta ce Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rantsar da sababbin kwamishinoni 19 da shugabannin hukumomi da kwamitoci a Benin City.

Kara karanta wannan

Bayan sauya sheka zuwa APC, Gwamna Mbah ya bijiro da bukatar sakin shugaban IPOB

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu a matsayinsa na mai kishin kasa.

Ya ce:

“Wannan ba zai faru ba da ba mu da shugaba mai kishin kasa, mun taba yin zabuka da dama a nan, kuma matsalar da muka sha fuskanta ita ce shugaba ba ya tare da mu.
"Amma yanzu muna cewa muna gode. Ba zan yafe wa kwamishina da bai sanya hular Asiwaju ba. Idan ka zo taro ba tare da wannan hula ba, sai ka koma gida."

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta dogara da farfaganda ba, sai dai aikatawa da sakamako da za a gani, yana mai cewa manufarsa ita ce taɓa rayuwar jama’a kai tsaye.

Gwamna ya yi gargadi ga mukarrabansa kan sanya hular Tinubu
Gwamna Monday Okpebholo yayin taro a birnin Benin City. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Source: Twitter

Tinubu: Gargadin Gwamna ga mukarrabansa

Okpebholo ya gargadi sababbin kwamishinoni da su guji cin hanci da rashawa, yana mai tuna musu cewa nadin da aka yi musu ba don tara dukiya ba ne, sai dai don yin hidima ga al’umma.

Kara karanta wannan

An fara guna guni da Majalisar Benue ta amince gwamna ya karbo bashin Naira biliyan 100

“Wannan gwamnati ba ta zo don ta yi ta surutu ba ne, sai dai aiki da sakamako mai gamsarwa a kowace al’umma.
“Ba don ku tara kuɗi aka ba ku wannan mukami ba. Ku zo ku yi aiki da sadaukarwa domin rayuwar al’ummar Edo ta inganta.
"Gwamnatina ba za ta lamunci rashawa ba, kuma za a auna ku da irin tasirin da kuka kawo wajen sauya rayuwar mutane."

- Monday Okpebholo

Gwamnan ya ƙara da cewa biyayyar kwamishinoni dole ne ya kasance ga jama’ar Edo, ba ga kowa ko jam’iyya ba, yana mai tuna musu cewa tarihi zai hukunta mu bisa ayyukanmu, ba niyyarmu ba.

Yayin taron an rantsar da shugabanni da mambobin Hukumar Ilimin Sakandare da Hukumar Gyaran Dokoki ta Edo, cewar Daily Post.

Gwamna ya dakatar da hadiminsa a Edo

A baya, kun ji cewa Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya dakatar da hadiminsa, Felix Isere bisa zargin haɗa kuɗaɗe ba tare da neman izini ba.

Okpebholo ya kuma kori Ahmed Musa daga matsayin shugaban hukumar EDOFEWMA tare da maye gurbinsa da Fashanu Emmanuel.

Kara karanta wannan

Bayan yafe wa mutum 175, Tinubu zai bada lambar girmamawa ga wasu kusan 1000

Wadannan matakai biyu sun fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Edo, Musa Ikhilor ranar Litinin, 28 ga watan Yuli, 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.