Tinubu Ya Shiga Wani Irin Yanayi bayan Mutuwar Malamin Addini a Najeriya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ta’aziyya bayan sanar da rasuwar babban malamin addinin Kirista a Najeriya
- Tinubu ya yi jimamin mutuwar Fasto Uma Ukpai, wanda ya kafa kungiyar 'Uma Ukpai Evangelistic' da kuma ba da gudunmawa sosai
- Ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin jajairtattu da suka ba da gudunmawa a bangaren bangaskiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kadu bayan samun labarin mutuwar daya daga cikin manyan malaman addini a Najeriya.
Tinubu ya yi jimami da alhini kan rasuwar fitaccen mai wa’azi kuma malamin addini, Fasto (Dr) Uma Ukpai.

Source: Twitter
Tinubu ya bayyana gudunmawar marigayi Ukpai
Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar a shafinsa na X a yai Talata 14 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin wanda ya kafa kungiyar 'Uma Ukpai Evangelistic; shi ne kuma ɗaya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN).
Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin jajirtattu da suka taka rawar gani wajen tayar da yada addini a Najeriya da sassan Afirka.
Tinubu ya ce:
“Cikin alhini na ke jajanta rasuwar ɗaya daga cikin jajirtattu, Dr Uma Ukpai. Ba malamin wa’azi kawai ba ne, amma mai albarka ne da cike da ƙaunar bishara, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen dawo da ɗabi’a, ƙauna, da zaman lafiya tsakanin mutane."
An haifi marigayi Ukpai a ƙaramar unguwar Asaga, Ohafia, a jihar Abia wanda ya rasu yana da shekara 80, ya kasance fitaccen mai bishara ta duniya
An tabbatar cewa Ukpai ya sha wahala wajen yin karatu, amma ya amsa kiran Ubangiji kuma ya yi tasiri mai zurfi ga al’umma ta hanyar aikinsa.
“Ya kasance ɗaya daga cikin rundunar masu wa'azi da suka ba da gudunmawa sosai na bishara a Najeriya da wasu sassan Afirka a shekarun 1980."
- Bola Tinubu

Source: Facebook
Tinubu ya yi addu'o'i bayan mutuwar Fasto
Shugaba Tinubu ya tuna da manyan tarukan addini da marigayin ya shirya, ciki har da wanda aka yi a 1982 da kuma a 1985, waɗanda suka yi tasiri sosai ta fuskar addini da zamantakewa.
Ya bayyana Fasto Ukpai a matsayin mai haɗa kan jama’a kuma mai tausayi, wanda ya gina makarantu, asibitoci da cibiyoyin agaji domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi, tare da inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai.
Ya kara da cewa:
“Ayyukansa sun haɗa mutane daban-daban, harsuna, da kabilu. Ya cika aikinsa na addini kuma ya koma ga Ubangiji, ya yi gwagwarmaya, ya kammala aikinsa, ya kiyaye bangaskiyarsa.
“Ina roƙon Allah Madaukaki ya sa ya huta na har abada, ya kuma ba iyalansa haƙuri da kwarin guiwa a wannan lokaci na tsanani."
Tinubu ya jajanta rasuwar tsohuwar minista
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna jimami bayan rasuwar tsohuwar Ministar Harkokin Waje ta Najeriya, Joy Uche Angela Ogwu.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
An sanar da rasuwar tsohuwar ministar wacce ta rike mukamin wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, ta cika ne ta na mai shekara 79.
Marigayiyar ta kasance wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya (UN) daga 2008 zuwa 2017, inda ta jagoranci Majalisar Tsaro ta UN sau biyu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

