Babban Albishir da Kashim Shettima Ya Yi Wa Yan Najeriya kan Halin Kunci

Babban Albishir da Kashim Shettima Ya Yi Wa Yan Najeriya kan Halin Kunci

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan halin kunci da yan kasa ke ciki musamman bayan daukar wasu matakai
  • Sanata Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kuncin tattalin arziki da ake kuka da shi zai ragu nan ba da jimawa ba
  • Ya ce gwamnati ta jawo zuba jari sama da dala miliyan 400 a masana’antar makamashin mai sabuntawa, wanda zai ƙirƙiri fiye da ayyuka 1,500

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana kwarin guiwa kan matakan da Bola Tinubu ke dauka a Najeriya.

Sanata Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kuncin tattalin arzikin da suke fuskanta a yanzu zai ragu nan ba da jimawa ba.

Kashim Shettima ya kwantarwa yan Najeriya hankali
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayin taro a Abuja. Hoto: Kashim Shettima.
Source: UGC

Shettima ya yi albishir ga 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Atiku: "Gaskiya ta fito da ministan Tinubu ya tona asiri kan kwangilar Legas zuwa Kalaba

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja yayin taronsu na ƙasa kan kirkire-kirkiren makamashin da ake sabuntawa, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya taron da nufin jan hankalin masu zuba jari a fannin masana’antar makamashin sabuntawa a cikin gida.

Ya bayyana cewa Najeriya na da damar zuba jarin fiye da dala biliyan 410 daga yanzu zuwa shekara ta 2060 a fannin makamashi.

Shettima ya ce:

“Zuciyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana tare da ‘yan Najeriya. Yana jin raɗaɗin da suke ciki, amma ku tabbata mun riga mun wuce ƙalubalen farko, yanzu muna kan hanya ta ci gaba da bunƙasa tattali.
“Fiye da Naira tiriliyan 23 ake bukata domin ƙara damar samar da wuta ga al’umma. Amma burinmu ya fi haka, muna son tsarin samar da wuta mai ƙarfin 277 'gigawatts' kafin shekarar 2060."
Shettima ya ce wahalar da ake sha zai zama tarihi
Kashim Shettima yayn jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Kokarin gwamnati kan inganta tattalin arziki

Shettima ya ce taken wannan taron na bana yana nufin ƙarfafa kera kayayyakin makamashi a cikin ƙasa, da haɓaka masana’antu na cikin gida domin Najeriya ta zama cibiyar makamashi ta Afirka.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Babban malamin addini ya riga mu gidan gaskiya

Ya bayyana cewa karkashin wannan shiri, an riga an jawo zuba jari sama da dala miliyan 400 a sassa daban-daban na masana’antar makamashin sabuntawa ciki har da kera wuta 'solar', ma'ajiyar baturi, da wuraren sake sarrafa kayan fasaha.

“Wadannan jarin za su samar da fiye da ayyuka 1,500 kai tsaye a jihohi da dama, kuma suna nuna yadda duniya ke da kwarin gwiwa kan manufofin Najeriya a fannin makamashi mai tsafta."

- Kashim Shettima

Ya ce manufar gwamnati ita ce a canza sakamakon taruka zuwa ayyukan gaske, wato gina masana’antu, samar da ayyuka, makarantu masu wutar lantarki, da ƙauyuka domin cigaba da samar da makamashi mai tsafta, cewar TheCable.

Wani dan kasuwa ya tattauna da Legit Hausa

Dan kasuwar magani, Abubakar Usman ya ce kullum fatansu kenan game da halin da ake ciki a Najeriya.

Ya ce:

"Tabbas ana bukatar sauki saboda idan akwai sauki a kayan masarufi komai zai tafi yadda ake so duk da farashin abinci ya ɗan sauka fiye da baya."

Usman ya ce amma a kullum cewa su ke yi saura kiris wanda yanzu ya fi shekara guda kenan inda ya yi addu'ar samun sauki nan ba sa jimawa ba.

Kara karanta wannan

2027: Majalisa ta yi wa 'yan Najeriya albishir kan gyaran dokar zabe

Shettima ya fadi matsayar Najeriya kan Falasdinu

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce Najeriya ta goyi bayan kiraye-kirayen da Birtaniya, Faransa da wasu kasashe ke yi na kafa kasar Falasdinawa.

Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana matsayar Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a Amurka.

Shettima, wanda ya wakilci Bola Tinubu, ya ce kafa kasar Falasdinu za ta kawo karshen rikicin Falasdinawa da Isra'ila.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.