Bayan Sauya Sheka zuwa APC, Gwamna Mbah Ya Bijiro da Bukatar Sakin Shugaban IPOB

Bayan Sauya Sheka zuwa APC, Gwamna Mbah Ya Bijiro da Bukatar Sakin Shugaban IPOB

  • Gwamna Peter Mbah da ya koma APC ya ce dole a warware batun Nnamdi Kanu ta sigar siyasa, ba kawai ta kotu ba
  • Ya bayyana cewa tun makon farko bayan hawansa mulki ya tattauna da Shugaba Bola Tinubu kan sakin Nnamdi Kanu
  • Mbah ya bukaci shugabannin Kudu maso Gabas su haɗa kai wajen neman mafitar siyasa ga matsalar shugaban IPOB

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu – Gwamnan jihar Enugu, Peter Ndubuisi Mbah, ya ce ya kamata a warware lamarin da ya shafi jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, ta hanyar siyasa maimakon dogaro da kotu kawai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa jama’ar jiharsa a ranar Talata, bayan ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gwamnan Enugu ya bukaci a yi amfani da siyasa wajen warware batun Nnamdi Kanu
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu lokacin da ake shigar da shi cikin kotu a Abuja. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Na yi maganar Kanu da Tinubu' - Gwamna

Kara karanta wannan

'Kowa ya bi': Gwamna ya umarci dukan mukarrabansa kan sanya hular Tinubu

Jaridar Punch ta rahoto gwamnan ya ce tun bayan hawansa mulki, ya tattauna da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan bukatar a saki Nnamdi Kanu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Peter Mbah ya ce:

“Kwana bakwai kacal bayan na hau mulki, na gana da shugaban kasa. Kuma na yi masa bayani kai tsaye cewa lallai dole ne a tattauna batun sakin Nnamdi Kanu."

Ya kara da cewa mafita ta siyasa ce hanya mafi dorewa domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Kudu maso Gabas.

“Na dade ina jaddada cewa za a iya magance matsalar Nnamdi Kanu ta sigar siyasa. Wannan wani lokaci ne ga yankinmu na mu haɗa kai mu nemi mafita mai dorewa."

- Gwamna Peter Mbah.

Kanu: Sakon gwamnan ga shugabannin Kudu

Gwamna Mbah ya bukaci shugabanni da dattawan Kudu maso Gabas su rungumi manufar warware lamarin Kanu ta siyasa kafin su gabatar da matsaya ga gwamnatin tarayya.

“Da farko, dole ne mu amince cewa wannan ita ce hanya mafi dacewa. Bayan haka sai a tsara cikakken tsarin aiwatarwa da za a gabatarwa gwamnati."

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An ji dalilin da ya sa gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

- Gwamna Peter Mbah.

Ya ce wannan batu ba abu ne da za a warware cikin gaggawa ba, amma dole ne yankin ya samu matsaya guda kafin a tunkari gwamnatin tarayya.

Gwamna Peter Mbah ya ce ya gana da Shugaba Bola Tinubu kan sakin Nnamdi Kanu
Gwamnan Enugu yana jawabi gaban Shugaba Bola Tinubu a Enugu. Hoto: @DanNwomeh
Source: Twitter

Nnamdi Kanu na tsare tun 2021

Zaman Nnamdi Kanu a hannun DSS tun daga watan Yuni, 2021, bayan an kama shi a Kenya kuma aka dawo da shi Najeriya, ya jawo cece-kuce daga shugabanni da kungiyoyi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana tsare Kanu a matsayin “tabo ga ƙasa”, yana mai kira da a sake shi cikin gaggawa.

Atiku ya bayyana cewa ci gaba da tsare jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB cin zarafi ne ga doka bayan kotu ta ba da belinsa, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Nnamdi Kanu ya tayar da kura a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, alkaliyar babbar kotun tarayya, Mai shari'a Binta Nyako, ta dage shari’ar Nnamdi Kanu ba tare da tsayar da ranar cigaba ba.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP a Enugu ya sauya sheka, ya hade da Tinubu a APC

A yayin wani zaman kotun da aka gudanar, Nnamdi Kanu ya nuna cewa bai yarda da alkalancin Binta Nyako ba, saboda ta riga ta janye kanta daga shari’ar.

Lauyan masu shigar da kara ya bukaci kotu ta sanya rana domin ci gaba da shari’a, amma alkaliyar ta dage shari’ar ba tare da wata tantama ko sanya rana ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com