An Yi Rashi a Yobe: Shugaban Hukumar Zabe Ya Yi Bankwana da Duniya

An Yi Rashi a Yobe: Shugaban Hukumar Zabe Ya Yi Bankwana da Duniya

  • An shiga jimami a Yobe sakamakon babban rashin da aka yi na daya daga cikin shugabannin hukumomi a jihar
  • Shugaban hukunar zabe mai zaman kanta ta Yobe, Dr. Muhammad Mamman, ya yi bankwana da duniya, inda ya rasu ya bar mata, 'ya'ya da jikoki
  • Marigayin ya rasu ne bayan ya yi fama da wata 'yar gajeruwar jinyar rashin lafiya, yayin da aka shirya sada shi da makwancinsa na karshe a ranar Talata, 14 ga watan Oktoba 2025

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Yobe - Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Yobe (YOSIEC), Dr. Muhammad Mamman, ya rasu.

Marigayi Dr. Muhammad Mamman ya yi bankwana da duniya ne bayan gajeriyar rashin lafiya.

Shugaban hukumar zaben Yobe ya rasu
Marigayi Dr. Muhammad Mamman. Hoto: Amir Mamman
Source: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Dr. Muhammad Mamman ya rasu ne a asibitin koyarwa na jihar Yobe da ke Damaturu.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An ji dalilin da ya sa gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar zabe a Yobe ya rasu

Marigayin ya rasu ya bar mata uku, ’ya’ya 33 da jikoki da dama a duniya.

Ɗaya daga cikin ’ya’yansa, Amir Muhammad, ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa, yana mai cewa marigayin ya mutu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.

“Ya rasu ya bar mata uku da yara 33 da jikoki, mun yi babban rashi. Ya rasu a asibitin koyarwa na jihar Yobe, Damaturu, kuma za a birne shi yau da misalin karfe 11:00 na safe."

- Amir Muhammad

Ya bayyana cewa jana’izarsa za ta gudana a babban Masallacin Juma’a da ke fadar Mai Martaba Sarkin Fika, Potiskum, jihar Yobe, da misalin karfe 11:00 na safe.

Marigayin, wanda likita ne a fannin lafiya, ya taɓa zama sakataren hukumar kula da asibitoci ta jihar Yobe a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Geidam.

Daga baya, Gwamna Mai Mala Buni ya nada shi a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Yobe (YOSIEC) sau biyu, kuma yana kan zaman wa’adinsa na karshe lokacin da ya rasu.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP a Enugu ya sauya sheka, ya hade da Tinubu a APC

Kafin rasuwarsa, Dr. Muhammad Mamman ya rike mukamin babban likitan masarautar Fika, inda daga baya aka ɗaukaka darajarsa zuwa Shamakin Fika.

Daya daga cikin 'ya'yansa, Amir Mamman, ya sanar da rasuwar mahaifin na sa a shafinsa na Facebook.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Cike da mika wuya ga nufin Allah Madaukakin Sarki, ina sanar da rasuwar mahaifina Dr. Muhammad Mamman. Allah Ya masa rahama."

- Amir Mamman

An yi rashin shugaban hukumar zaben jihar Yobe
Taswirar jihar Yobe, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi ta'aziyyar rasuwar marigayin

Muhammad Dauda:

"Allah ya jikansa da rahama yasa aljanna fiddausi ce makomarsa."

Idriss Abba:

"Allah ya jikansa da rahama yasa aljanna fiddausi ce mako marsa"

Yusra Musadiq:

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah yajikansa, Allah yamasa rahama, Allah ys mutuwa hutune
Ameeeeen."

G Muhammad Abubakar Abdullahi:

"Inna lillahi wa Inna ilaihi raju'un Allah ya gafarta masa da Rahamarsa, Allah ya baku hakuri da juriyan rashinshi. Sannun ku da hakuri abin akwai zafi."

Tsohuwar Minista ta rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohuwar ministar harkokin waje Joy Uche Angela Ogwu ta yi bankwana da duniya.

Kara karanta wannan

Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu

Marigayiya Joe Uche Angela ta rasu ne tana da shekara 79 a duniya, inda kafin rasuwarta ta bada gudunmawa sosai ga Najeriya.

Joe Uche Angela wadda take masaniya kan harkokin kasashen waje da malamar kimiyya, ta taba zama shugabar cibiyar harkokin kasashen waje ta Najeriya (NIIA).

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng