Kwana Ya Kare: Tsohuwar Minista a Najeriya Ta Yi Bankwana da Duniya
- Najeriya ta sake yin babban rashi bayan sanar da rasuwar tsohuwar minista wacce ta rike mukamin wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna jimami kan rasuwar Joy Uche Angela Ogwu, tsohuwar Ministar Harkokin Waje ta Najeriya mai shekara 79
- Marigayiyar ta kasance wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya (UN) daga 2008 zuwa 2017, inda ta jagoranci Majalisar Tsaro ta UN sau biyu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — An shiga jimami a Najeriya bayan rasuwar tsohuwar minista a ma'aikatar harkokin wajen kasar wacce ta ba da gudunmawa sosai.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jimami kan rasuwar Joy Uche Angela Ogwu wacce ta rasu tana da shekaru 79 a duniya.

Source: Facebook
Tsohuwar minista ta riga mu gidan gaskiya
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Facebook na hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga a yau Talata 14 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayiwa Ogwu ta yi aiki a matsayin Jakadiya kuma wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya (UN) a birnin New York daga Mayu 2008 zuwa Mayu 2017, inda ta wakilci ƙasar cikin ƙwarewa da jajircewa.
A matsayinta ta masaniya kan harkokin kasashen waje da malamar kimiyya, ta taba zama Daraktar Janar na Cibiyar Harkokin Ƙasashen Waje ta Najeriya (NIIA).
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ta taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka manufofin ƙasar a fannin hulɗar ƙasashen waje da nazarin dangantaka tsakanin ƙasashe.
Ta kuma jagoranci Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya sau biyu a Yuli 2010 da Oktoba 2011, abin da ya tabbatar da girmamawar da duniya ke mata.

Source: Facebook
Abin da Tinubu ya ce kan rasuwar marigariyar
A cikin sanarwa da Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba da irin gudunmawar da marigayiyar ta bayar wajen ɗaga darajar da matsayin Najeriya a duniya, tare da nuna kishinta ga zaman lafiya, tsaron duniya, da ‘yancin mata.
“Najeriya ta yi babban rashi. Mun rasa gwarzuya da ta kai kololuwar aikinta ta hanyar ƙwazo, jajircewa da ƙwarewa."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga ‘ya’yanta biyar, jikokinta, ‘yan uwanta mata da maza, da dukkan dangin Ogwu, tare da al’ummar kasashen duniya da bangaren ilimi da ke jimamin wannan rashi.
Ya yi addu’ar Allah Ya jikanta da rahama, ya kuma ba iyalanta da abokan aikinta haƙuri da ƙwarin guiwa wajen jure wannan babban rashi.
Tsohon Jakada ya rasu yana da shekaru 92
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi da muke samu sun tabbatar da rasuwar tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya ranar Laraba 8 ga watan Oktoban 2025.
An shiga jimami bayan rasuwar Dr Christopher Kolade, yana da shekaru 92 da haihuwa, kamar yadda iyalansa suka bayyana cikin tausayi da kuma godiya da irin rayuwar da ya yi.
Iyalansa sun ce tsohon shugaban 'Cadbury Nigeria' ya rasu cikin aminci a ranar Laraba, bayan cikar Najeriya 65 da samun 'yanci inda suka bayyana irin gudunmawa da ya ba kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

