Ana Wata ga Wata: Majalisa na Son Dawo da Zaben 2027 zuwa 2026
- Majalisar dokokin Najeriya na shirin sauya lokacin gudanar da babban zabe zuwa Nuwamban 2026 maimakon Fabrairun 2027
- An bayyana shirin ne a zaman jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Abuja kan kudirin gyaran dokar zabe ta shekarar 2025
- Sabon tsarin zai tabbatar da kammala karar zabe kafin ranar 29 ga Mayun 2027, lokacin mika mulki ga sabuwar gwamnati a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Majalisar dokokin Najeriya ta fara shirin canza lokacin gudanar da babban zaben kasar.
Matakin yana cikin kudirin gyaran dokar zabe ta shekarar 2025, wanda aka gabatar a taron jin ra’ayin jama’a da kwamitocin zabe na majalisar dattawa da na majalisar wakilai suka shirya.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa an ce sabon tsarin na da nufin samar da isashen lokacin kammala dukkan karar da ta shafi zabe kafin ranar 29, Mayu, 2027.
Dalilin neman sauya ranar zabe
Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dokokin Najeriya na neman dawo da zaben Najeriya watan Nuwamban 2026 maimakon Fabrairun 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin harkokin zabe na majalisar, Hon. Adebayo Balogun, ya ce an dauki matakin ne don tabbatar da cewa duk shari’o’in zabe sun kare kafin a rantsar da sababbin shugabanni.
Majalisar na son gyara sassa na 285 da 139 na tsarin mulkin 1999, don rage wa’adin yanke hukunci a kotunan zabe daga kwana 180 zuwa 90 da kuma na kotunan daukaka kara daga 90 zuwa 60.
A cewarsa, wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa ba a wuce kwanaki 185 kafin kammala dukkan matakan shari’a bayan kammala zabe.
Shawarwari a kudirin gyaran zabe
Daya daga cikin muhimman abubuwan da kudirin ya tanada shi ne ba da damar yin zabe ga wasu rukuni na ‘yan kasa kamar jami’an tsaro, ma’aikatan INEC, manema labarai da masu lura da zabe.
Kudirin ya kuma bukaci tilasta amfani da tsarin aikawa da sakamakon zabe ta yanar gizo da kuma a rubuce, tare da hukunta duk wanda bai bi ka’ida ba.
Wani sashe na kudirin ya ce dole jami’in zabe dole ya tura sakamakon zabe da adadin masu kada kuri’a.

Source: Facebook
Haka kuma, duk jami’in da ya bayar da takardun kuri’a ko sakamakon da ba su da hatimi zai fuskanci dauri na shekara 10 ko tara har Naira miliyan 1.
Ra’ayoyin masu ruwa da tsaki
Jami’an Hukumar Zabe ta Kasa da Farfesa Abdullahi Zuru ya wakilta, sun bayyana goyon bayansu ga wannan kudiri, musamman kan amfani da tsarin yanar gizo wajen gudanar da zabe.
Jaridar This Day ta wallafa cewa sun ce hakan zai karfafa amincewar jama’a da sakamakon zabe da kuma rage yawan rigingimun bayan zabe.
ADC ta yi kira ga shugaban INEC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi kira ga sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan. Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya yi kira ga sabon shugaban da ya yi adalci wajen gudanar da zaben 2027.
Bolaji Abdullahi ya bukaci Farfesa Amupitan da ya kasance mai biyayya ga Najeriya ba gwamnati da ta nada shi shugaban INEC ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
