Gwamnatin Tarayya Ta Fusata kan Yajin Aikin ASUU, Ta Ba Shugabannin Jam'i'o'i Umarni
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta tsunduma yajin aikin gargadi na makonni biyu a fadin kasar nan
- Gwamnatin tarayya ta nuna rashin jindadinta kan matakin da kungiyar ASUU ta dauka na shiga yajin aikin
- Ministan ilmi ya bada umarni ga shugabannin jami'o'i kan matakin da za su dauka ga malaman da suka shiga yajin aikin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU), ta shiga a fadin kasar nan.
Gwamnatin ta umarci shugabannin jami’o’i da su tabbatar da aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga dukkan mambobin ASUU da suka shiga yajin aiki.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da Ministan ilmi, Farfesa Tunji Alausa, ya aika zuwa ga shugabannin jami'o'in.

Kara karanta wannan
Gwamna ya kwantar da hankalin 'yan PDP kan yawan ficewa daga jam'iyyar, ya yi albishir
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai gwamnati ta keɓe mambobin kungiyoyin CONUA da NAMDA daga wannan umarni, saboda ba su shiga yajin aikin ba.
Mambobin ASUU sun shiga yajin aiki
Mambobin ASUU sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki 14 a jiya Litinin, duk da rokon da gwamnati ta yi kan su yi haƙuri, ganin cewa ta amince da mafi yawan bukatunsu da ke karkashin ikon ta.
Kungiyoyin CONUA da NAMDA kuwa sun bayyana cewa ba su da hannu a yajin aikin da ASUU ta shiga domin nunawa gwamnati fushinta.
NAMDA ta kunshi malaman asibiti da ke koyarwa a jami'o'i yayin da CONUA ta fito domin kishiyantar kungiyar ASUU da aka kafa a 1978.
Me gwamnati ta ce kan yajin aikin ASUU?
Ministan ilmi, Tunji Alausa, ya nuna rashin jin daɗi kan matakin na ASUU, inda ya umarci shugabannin jami’o’i da su gudanar da kirgar malamai da suke halartar aiki.
Ya kara da cewa hukumar jami’o’i ta kasa (NUC) za ta sa ido kan yadda jami’o’in ke bin wannan umarni tare da tattara rahoto na musamman domin mika shi ma’aikatarsa, rahoton tashar Channels tv ya kawo zancen.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kebbi ta tsage gaskiya kan batun 'yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar
A cikin wasikar da ya aikewa shugabannin jami’o’i, Alausa ya bayyana cewa gwamnati ta ji takaici matuka ganin ASUU ta fara yajin aiki duk da kiran da ake ta yi gare su da su rungumi tattaunawa mai ma’ana domin samun maslaha mai ɗorewa.
"Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na nuna rashin gamsuwa da rahotannin da ke nuna cewa ASUU ta shiga yajin aiki duk da kiran da aka yi a gare ta da ta rungumi tattaunawa, wacce ita ce hanya mafi tasiri da dorewa wajen warware matsalolin da ke addabar fannin ilmin jami’a.”
"Bisa tanadin dokokin kwadago na kasa, Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada matsayinta kan aiwatar da dokar ‘Ba aiki, ba albashi’ ga duk wani ma’aikaci da ya gaza yin aikinsa yayin yajin aiki.”
- Tunji Alausa

Source: Facebook
Hakazalika ministan ya umarci shugabannin jami’o’i da su dakatar da biyan albashi ga duk malamin da bai halarci ofis ba a lokacin yajin aikin.
Gwamnati ta roki kungiyar ASUU
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bukaci kungiyar ASUU da ta hakura da shirin shiga yajin aiki.
Gwamnatin ta ba kungiyar ASUU tabbacin cewa ana aiki tukuru don warware duk buƙatun da ta gabatar sannu a hankali.
Ministan ilmi, Tunji Alausa ya bayyana cewa an sake kafa Kwamitin Mahmud Yayale Ahmed da ke tattaunawa da manyan cibiyoyin ilimi domin a samu mafita.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
