Amaechi Ya Samo Mafita ga Gwamnati kan Matsalar Rashin Tsaro
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya tabo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya
- Rotimi Amaechi ya nuna cewa matsalar rashin tsaro ba abu ba ne wanda za a iya magancewa ta hanyar amfani da jami'an tsaro kadai ba
- Tsohon ministan ya bayyana cewa dole ne gwamnatin da take son yaki da rashin tsaro ta fara magance matsalar yunwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.
Rotimi Amaechi ya ce yaki da rashin tsaro ba zai haifar da sakamako mai kyau ba muddin gwamnati ba ta magance matsalar yunwa a tsakanin ‘yan kasa ba.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce Amaechi ya faɗi haka ne a ranar Lahadi yayin wani taron tattaunawa ta yanar gizo da matasan jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan
An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Amaechi ya ce kan rashin tsaro?
Ya ce dogaro kawai da karfin soja ko ‘yan sanda wajen yaki da rashin tsaro ba tare da magance talauci da yunwa ba, na kara haifar da rikice-rikice da rashin kwanciyar hankali a kasar nan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.
"Dole ne duk wani shugaba da ke son warware matsalar rashin tsaro a Najeriya, ya gane cewa tsauraran matakan tsaro kaɗai ba za su wadatar ba."
“Ko da kuwa an tanadar wa sojoji da ‘yan sanda kayan aiki sosai, sauran mutane za su ci gaba da neman makamai don su rama ko su kare kansu daga jami’an gwamnati.”
- Rotimi Amaechi
Matakin da Amaechi ya dauka a Rivers
Amaechi ya tuna cewa a lokacin da yake gwamnan jihar Rivers, gwamnatinsa ta yi amfani da doka, ta karfafa hukumomin tsaro, ta inganta haɗin kai tsakaninsu, tare da kyautata rayuwar al’umma domin rage laifuffuka.
"Da muka hau mulki, mun fara gina makarantun firamare a kowane kauye, gina cibiyoyin lafiya na matakin farko, da kuma buɗe hanyoyi zuwa yankunan karkara."
“Amma ba wannan kaɗai ba, mun tabbatar da cewa kwangilolin aikin suna hannun ‘yan kauyen da ake aikin a cikinsu."
"Idan aka biya su, suna biyan ma’aikata, kuɗin kuma suna yawo a cikin al’umma. Wannan ya samar da ayyukan yi, ya hana mutane zaman banza, ya rage aikata laifi.”
“Mun fara samar da hanyoyin halas na samun abin yi kafin mu tsaurara doka. Mutane suka gane cewa duk wanda ya shiga garkuwa da mutane ko ta’addanci mai karya doka ne, ba mai fafutukar neman ‘yanci ba."
"Ba za ka iya sanyawa yunwa jami'an tsaro ba, za ka gina zaman lafiya ne idan mutane suna da aiki, suna da mutunci, kuma suna da amincewa kan gwamnati."
- Rotimi Amaechi

Source: Twitter
Amaechi ya magantu kan takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan shirin fitowa takara a zaben shekarar 2027.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan burinsa na hawa kan madafun ikon kasar nan.
Tsohon gwamnan ya dole ne zaben fitar da gwani na ADC ya kasance an ba kowa dama, inda ya kara da cewa ba zai janye wa kowanne ɗan takara ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

