Gwamnatin Kebbi Ta Tsage Gaskiya kan Batun 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari a Jihar
- Gwamnatin jihar Kebbi ta fita ta yi magana kan wasu rahotannin da ke cewa 'yan bindiga sun kai kazamin hari a karamar hukumar Sakaba
- Wasu rahotannin da aka yada dai sun yi ikirarin cewa 'yan binddga sun yi barna mai yawa a wani hari da suka kai a kauyen Makuku
- Sai dai, a cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta yi bayani dalla-dalla kan rahotannin tare da bayyana ainihin inda aka kai harin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta karyata rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Makuku da ke karamar hukumar Sakaba.
Gwamnatin Nasir Idris ta bayyana cewa labarin karya ne kuma an yada shi ne don yaudarar jama’a.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, ya fitar a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025.
Rahoton da wani gidan rediyo na FM a Birnin Kebbi ya yada, ya yi ikirarin cewa an kashe mutane da dama a wani mummunan harin 'yan bindiga da aka ce ya auku a yankin.
Me gwamnatin Kebbi ta ce kan harin 'yan bindiga?
A cewar gwamnatin jihar, musanta labarin wani ɓangare ne na kokarinta wajen yaki da yaɗa karya da jawo tashin hankali.
Gwamnatin ta kwantar wa jama’a hankali yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ayyukansu na kokarin samar da tsaro.
Sakataren yada labaran gwamnan ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Rijau, wani yanki da ke cikin jihar Neja mai makwabtaka da Kebbi.
Ya jaddada cewa babu wani hari irin wannan da ya faru a cikin jihar Kebbi.
"Babu irin wannan lamari a Kebbi. An yada rahoton don yaudarar jama’a ne kuma yana iya jawo tashin hankali."
- Ahmed Idris
Wane mataki gwamnati ke dauka kan tsaro?

Kara karanta wannan
Majalisar Kolin Musulunci ta karyata batun kisan Kiristoci, ta caccaki CAN, Tinubu
Ya kara da cewa gundumar Sakaba tana da sansanin soja da gwamnatin jihar ta kafa, wanda hakan ya karfafa tsaro a yankin, rahoton Daily Post ya tabbatar da labarin.

Source: Original
A karshe, Ahmed Idris ya roki jama’ar jihar su yi watsi da rahoton na karya, sannan su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Hakazalika ya tabbatar da cewa an ba jami’an tsaro cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a dukkanin faɗin jihar.
'Yan bindiga sun kai hari a Nasarawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
'Yan bindigan sun hallaka mutane tara ciki har da wadanda suka yi wa yankan rago a kazamin harin wanda suka kai a karamar hukumar Kokona ta jihar.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kai gawarwakin mutanen da aka kashe zuwa dakin ajiye gawa, kuma binciken farko ya nuna cewa harin na iya zama mai nasaba da rikicin filaye da ya daɗe a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
