Edun: Rashin Lafiya Ya Kama Ministan Tinubu, Ya Gaza Wakiltar Najeriya a Amurka
- Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF
- Ministan kudi, Wale Edun, ba zai halarci taron ba saboda rashin lafiya, inda Cardoso zai maye gurbinsa a taron da za a yi a kasar Amurka
- Taron zai gudana daga ranar 13 zuwa 17, Oktoba, 2025, tare da tattaunawa kan ci gaban kasa, tattalin arziki, da kasuwannin kudi a fadin duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da taron ne a birnin Washington DC na Amurka daga ranar Litinin, 13, Oktoba, 2025.

Source: Getty Images
Legit ta gano hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a X.

Kara karanta wannan
An gano tsofaffin shugabannin Najeriya 3 da ba su halarci taron majalisar koli ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Onanuga ya bayyana cewa Cardoso zai wakilci Ministan Kudi, Wale Edun, wanda ke fama da rashin lafiya.
Sanarwar ta ce tawagar Najeriya za ta hada da karamar ministan kudi, Doris Uzoka-Anete, wacce za ta kasance cikin mahalarta muhimman zaman tattaunawa da Bankin Duniya da IMF.
Gwamnan CBN ya maye gurbin ministan kudi
A cewar sanarwar, Cardoso, wanda shi ne gwamnan bankin Najeriya, zai maye gurbin Minista Wale Edun, wanda ba zai iya halartar taron saboda rashin lafiya ba.
An bayyana cewa, Edun na karbar kulawar likitoci a Najeriya, sai dai idan bukatar ta taso, ana iya kai shi waje domin samun cikakkiyar kulawa.
Rahoton the Gurdian ya ce shugaban kasa Bola Tinubu na iya duba yiwuwar nada sabon ministan kudi idan jinyar Edun ta dauki lokaci mai tsawo.
Ana hasashen yin haka ne kasancewar yana daga cikin ginshikan tawagar tattalin arzikin gwamnati tun daga watan Agusta, 2023.
Abubuwan da za a tattauna a taron Amurkan
A cewar Bankin Duniya, taron shekara-shekara zai kunshi zaman kwamitin ci gaban kasa a ranar Alhamis, 16, Oktoban 2025.
Baya ga haka, bankin duniya ya sanar da cewa za a yi zaman kwamitin lamunin kudi na kasa da kasa a ranar Juma’a, 17, Oktoban 2025.

Source: Twitter
Baya ga wannan, za a gudanar da taruka na musamman, hira da manema labarai, da kuma tattaunawa kan ci gaban tattalin arziki, harkokin kudi, da kasuwannin duniya.
Taron na daga cikin muhimman lokutan da ke bai wa kasashe damar musayar ra’ayi kan hanyoyin bunkasa tattalin arziki da jawo masu zuba jari daga kasashen waje.
An nada Edun a matsayin ministan kudi da harkokin tattalin arziki a watan Agustan 2023, a matsayin wani jigo na bangaren sababbin gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ke son yi.
Shugaba Tinubu ya tafi kasar Italiya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi birnin Roma na kasar Italy.
Tuni shugaban kasar ya isa Italy a yammacin ranar Lahadi kamar yadda rahoton fadar shugaban kasa ya tabbatar.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai tattauna ne kan muhimman abubuwa da suka shafi tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

