Karshen Damina: Ruwan Sama Zai Sauka a Kebbi, Bauchi da Wasu Jihohi Gobe Litinin
- Taraba, Adamawa, Kaduna, Borno, Gombe, Kebbi, da wasu jihohin Arewa za su samu ruwan sama a gobe Litinin, 12 ga Oktoba, 2025
- NiMet ta yi gargadin cewa ruwan sama da iska za su iya rage ganin masu tuka ababen hawa, kuma santsin titi zai iya jawo hadurra
- An kuma shawarci wadanda ke zaune a yankunan da suka saba fuskantar ambaliya su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kamar yadda ta saba a kullum, hukumar NiMet ta fitar da hasashen yanayi na ranar Litinin, inda ta ce za a samu ruwan sama a sassan kasar nan.
Hasashen yanayin ya nuna cewa za a samu ruwan sama a wasu jihohin Arewa, ciki har da Taraba, Kebbi, da sauransu, yayin da damina ke bankwana.

Kara karanta wannan
An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu

Source: Original
Hasashen yanayin na ranar Litinin na kunshe ne a cikin sanarwar da NiMet ta fitar a shafinta na X a daren ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, 2025.
Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa
A safiyar Litinin, NiMet ta ce za a samu rana, sai kuma jefi-jefi na hadari, sannan za a iya samun ruwan sama da iska a wasu sassan jihohin Taraba da Kudancin Kebbi.
Da yammaci zuwa dare kuwa, NiMet ta ce za a samu saukar ruwan sama mai matsakaicin karfi a jihohin Taraba, Adamawa, Kaduna, Borno, Bauchi, Gombe, Kebbi, da Kudancin Sokoto.
Da hukumar ta leka shiyyar Arewa ta Tsakiya, ta rahoto cewa za a samu rana, sannan ruwan sama mai matsakaicin karfi na iya sauka a jihohin Niger, Benue, Plateau, da Kogi.
Hasashen ruwan sama a Kudu
Daga yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran iska mai karfi hade da ruwan sama za su sauka a sassan Babban birnin tarayya Abuja da jihohin Niger, Kogi, Kwara, da Nasarawa.
A Kudancin Najeriya kuwa, ana hasashen ruwan sama mai matsakaicin karfi zai sauka a jihohin Ogun, Ondo, Ekiti, Imo, Ebonyi, da Abia, kuma rana za ta fito.
Sannan da yammaci zuwa dare, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin karfi hade da iska zai sauka a kusan dukkanin jihohin shiyyar.

Source: Original
Shawarwari da gargadin NiMet
Bayan fitar da hasashen yanayin, NiMet ta kuma ba da shawarwari gami da gargadi ga 'yan Najeriya kamar yadda saba, cewa:
Iska mai karfi za ta iya kawo tsaiko ga ayyukan yau da kullum da jama'a suka saba yi a waje.
Ruwan sama da iska za su iya rage ganin masu tuka ababen hawa, kuma santsin titi zai iya jawo hadurra, don haka direbobi su yi hattara.
Wadanda ke zaune a yankunan da suka saba fuskantar ambaliya su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyinsu.
An shawari hukumomin gwamnati, musamman ba su kai dauki da ba da agajin gaggawa, masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Gidajen mutane da gonaki sun nutse cikin ruwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya ta mamaye gidaje, tituna, gonaki da shaguna a jihar Anambra.
Mazauna yankunan da ambaliyar ta shafa, sun gaggauta tattara ya-nasu ya-nasu sun fice daga gidajensu don tsira da rayukansu.
Kwamishinan muhalli na jihar Anambra, Felix Odimegwu ya bayyana irin matakan da gwamnatin Anambra ta dauka kan ambaliyar.
Asali: Legit.ng

