Kebbi: 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa bayan Kai Mummunan Hari, Sun 'Fille' Kan Sarki

Kebbi: 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa bayan Kai Mummunan Hari, Sun 'Fille' Kan Sarki

  • 'Yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Makuku, karamar hukumar Sakaba, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutane da dama
  • Shaidu sun ce maharan sun shiga da daddare suna harbi, sun kona gidaje da fasa shaguna kafin su gudu da mutane da dukiyoyi
  • Rahotanni sun tabbatar cewa ‘yan bindigar sun hallaka Sarkin Hausawan garin wanda ya tayar da hankulan al'umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sakaba, Kebbi - An shiga halin tashin hankali bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a garin Makuku da ke karamar hukumar Sakaba a jihar Kebbi.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun mamaye garin da tsakar dare suna harbe-harbe tare da kona gidaje da kashe mutane da dama.

Yan bindiga sun hallaka Sarki a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Bakatsine da ke kawo bayanai kan tsaro ya ce maharan sun sace wasu mazauna yankin tare da kwashe kayayyaki wanda ya firgita al'ummar yankin.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a jihar Benue, an yi asarar rayuka kafin zuwan sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kebbi: Yadda ake fama da hare-haren yan bindiga

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsanancin rashin tsaro da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Jami'an tsaro da hadin guiwar yan sa-kai na ba da gudunmawa wurin ganin an kawo karshen hare-haren da ake kaiwa.

Ko a kwanakin baya, wani dan sa-kai ya tayar wa al’umma hankali bayan ya budewa mutane wuta a cikin masallaci a jihar Kebbi.

Lamarin ya tayar da hankukan al'ummar yankin Faransi a karamar hukumar Danko Wasagu da ke jihar.

Rahotanni sun ce an garzaya da matashin da aka ji wa rauni mai suna Bawa Kiri asibitin Ribah a Zuru domin kulawar likitoci.

Yan bindiga sun yi ta'adi a jihar Kebbi

Majiyoyi suka ce yan ta'addan sun sace abinci daga shagunan mutanen da suka kai musu hari bayan balle su wanda ya jawo asarar miliyoyin kudi a yankin.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

A wani abu mai tayar da hankali, rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yanke kan Sarkin Hausawan garin kafin su tsere.

Wasu yan bindiga sun yanke kan Sarki a Kebbi
Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Defense Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Wane martani hukumomin tsaro suka yi?

Hukumomin tsaro dai ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.

Sanarwar ta ce:

"A daren jiya, ‘yan ta’adda da ake kira da ‘yan bindiga sun kai hari a garin Makuku da ke karamar hukumar Sakaba, Jihar Kebbi.
"An kashe mutane da dama, wasu kuma an sace su tare da fasa shaguna da dama.
"Rahotanni sun ce maharan sun yanke kan Sarkin Hausawan garin kafin su tsere."

Miyagu sun fille kan tsohuwa a Anambra

Mun ba ku labarin cewa yan sanda a jihar Anambra sun kama Obadigbo Emmanuel Anumudu da ake zargi da kisan gilla ga wata mata mai shekara 69.

An kama shi ne bayan shekara guda da ya gudu daga yankin Umueri, inda aka kashe Obianuju Akubi a watan Yulin shekarar 2024.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta ce bincike yana ci gaba da gudana domin kama sauran masu hannu a laifin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.