Rayuwar Dubban Matasa Za Ta Sauya, an Tallafa Musu bayan Koyon Sana’o’i, APC Ta Yi Magana
- Gwamna Hope Uzodinma ya tuna da matasa a Imo makwanni bayan Bola Tinubu ya ziyarci jihar domin kaddamar da ayyuka
- Uzodinma ya horar da matasa 50,000 a jihar ta hanyar shirin 'SkillUp' Imo domin ba su ƙwarewar zamani da inganta rayuwarsa
- Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba da shirin, yana cewa Gwamnan ya farfaɗo da bege a zukatan matasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owerri, Imo — Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya cika burinsa na horar da matasa domin bunkasa rayuwarsu a jihar.
Gwamna Uzodinma ya horas da matasa 50,000 a fannin fasahar zamani ta hanyar shirin 'SkillUp Imo Project' wanda aka yi a birnin Owerri.

Source: Twitter
Gwamna Uzodinma ya horas da matasa 50,000
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin X na hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu, Sunday Dare a yau Lahadi 12 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa wannan lamari ya zama gagarumin shiri na kawo cigaba ga matasa a jihar inda aka yabawa gwamnan kan haka.
Shirin, wanda ke ƙarƙashin 'Imo Digital Economy Agenda' (iDEA 2022–2026), yana nufin tabbatar da fasaha a matsayin tushen cigaban tattalin arziki a jihar Imo.
A yayin bikin kammala horo na rukuni na uku, matasa 10,000 sun kammala karatun kwasa-kwasai na musamman a fannoni da dama ciki har da haɓaka manhajoji.
Sannan akwai wadanda suka samu horaswa a nazarin bayanai, tsaron yanar gizo, kasuwancin yanar gizo da gyaran wayoyi da kwamfutoci.

Source: Twitter
APC ta yabawa Gwamna Hope Uzodinma a Imo
A jawabinsa yayin bikin, Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba ƙwarai da Gwamna Uzodinma bisa hangen nesan da ya nuna wajen ƙarfafa matasa a fannin fasaha.
“Na ji daɗi ƙwarai, na burge. Kun farfaɗo da bege a zukatan matasa — ba abin mamaki ba ne sun kira ka Hope.”

Kara karanta wannan
Malami ya yi hasashen mai nasara a zaben 2027, ya ce gwamna zai taka wa Tinubu birki
- Nentawe Yilwatda
A nasa jawabin, Gwamna Hope Uzodinma ya bayyana cewa shirin yana nuna hangen nesansa na ganin matasan Imo sun shiga sahun gaba a duniyar fasahar zamani.
Ya ce:
“Burinmu shi ne mu sanya Imo a gaba a fannin tattalin arzikin dijital. Na yi alfahari da ƙara matasa 10,000 zuwa cikin 40,000 da aka riga aka horar — yanzu sun zama 50,000.
“Muna gina Imo inda hanyar da za ta zama kamar hanyoyin mota — a ko’ina."
Gwamnan ya kuma gode wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa manufofinsa na ƙarfafa tattalin arzikin jihohi da ƙara yawan kuɗin shiga.
Tinubu ya kai ziyarar aiki a Imo
A wani labarin, Bola Tinubu ya samu rakiyar jiga-jigan APC da sauran siyasa da suka raka shi zuwa jihar Imo domin kaddamar da ayyuka.
Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tsofaffin shugabannin APC biyu, Adams Oshiomhole da Abdullahi Umar Ganduje suna daga cikin mahalarta bikin.
Har ila yau, akwai gwamnonin jihohin APC, tare da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, wadanda suka halarci kaddamar da ayyukan da kuma ƙaddamar da littafi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

