An Samu Karancin Man Fetur a Arewacin Najeriya, Lita Ta Haura N960 a Jihar Sokoto

An Samu Karancin Man Fetur a Arewacin Najeriya, Lita Ta Haura N960 a Jihar Sokoto

  • Duk da janye yajin aikin PENGASSAN, karancin man fetur ya ci gaba da addabar Sokoto, inda gidajen mai da dama suka rufe baki ɗaya
  • An rahoto cewa ana sayar da lita ɗaya tsakanin ₦960 zuwa ₦970, yayin da a kasuwar bayan fage farashin lita ya kai har ₦1,250
  • Jama’a sun bukaci gwamnatin Sokoto da DPR su tilasta masu gidajen mai su dawo da aiki domin rage wahalar sufuri da tsadar rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto – Duk da janye yajin aikin da ƙungiyar PENGASSAN ta yi, matsalar karancin fetur ta ci gaba da addabar jihar Sokoto, inda ta janyo tsadar sufuri da cunkoson jama’a a gidajen mai.

Rahotanni sun bayyana cewa an rufe yawancin gidajen mai, yayin da kaɗan daga cikin wadanda aka bude suke sayar da lita tsakanin ₦960 zuwa ₦970.

Kara karanta wannan

Daga faduwa zaben cike gurbi, dan takarar jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC

An samu karancin man fetur a Sokoto duk da PENGASSAN ta janye yajin aiki
Mutane sun yi layin sayen fetur a wani gidan sayar da mai. Hoto: Getty Images
Source: UGC

An tattara wannan rahoto ne bayan ziyarar da wakilin jaridar The Punch ya kai wasu gidajen mai a cikin birnin Sokoto a ranar Juma’a.

Man fetur ya yi tsada a jiha Sokoto

A kasuwar bayan fage kuwa, ana sayar da lita ɗaya har ₦1,250, yayin da jarka mai cin lita huɗu ke kai ₦6,000.

An rahoto cewa wannan ya tilasta wa direbobi da masu ababen hawa da dama ajiye motocinsu, suka koma amfani da adaidaita sahu (Keke NAPEP) da babura don yin zirga-zirga.

Wani direba mai suna Mallam Abba Umar ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ‘yan kasuwa ke ƙirƙirar karancin man fetur don ƙara farashi.

“Yawancin masu gidajen mai a Sokoto makiya jama’a ne. Suna da mai amma ba sa sayarwa da rana. Suna buɗe wa da daddare ne kawai su sayar a farashi mai tsada. Ya kamata gwamnati ta ceci jama’a daga wannan wahala."

- Mallam Abba Umar.

Kara karanta wannan

Mutanen da suka ja junnen Jonathan game da sake neman mulkin Najeriya a 2027

Gidajen man NNPC ba sa sayarwa da fetur

Wakilin jaridar ya gano cewa wasu gidajen mai na NNPC guda bakwai a cikin birnin Sokoto su ma sun daina sayar da man fetur a lokacin da aka tattara wannan rahoto.

Wannan matsalar ta janyo tituna sun yi tsit, dogayen layuka a kaɗan daga cikin gidajen mai da ke aiki, da kuma tsadar kuɗin abun hawa, abin da ya ƙara wahalar da rayuwar jama’a.

Wani direban mota, Usman Bello, ya koka cewa tsadar mai ta hana su samun riba.

“Da na kan sayi man ₦10,000 ne kawai a rana, amma yanzu har na ₦20,000 ba ya isa ta."

- Usman Bello.

An rahoto cewa 'yan bumburutu na cin karensu ba babbaka a Sokoto saboda karancin man da aka samu
Hoton 'yan bumburutu suna sayar da man fetur a gefen hanya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jama’a na neman gwamnati ta dauki mataki

Mazauna Sokoto sun roƙi gwamnatin jihar, da hukumar DPR, da kuma hukumomin tarayya da su hanzarta daukar mataki domin tilasta masu gidajen mai su koma aiki yadda ya dace.

Sun kuma bukaci kamfanin NNPCL Ya ƙara isar da man fetur zuwa yankin don rage radadin da jama’a ke ciki da dawo da al’amura yadda suka saba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun samu nasara kan mutanen da ake zargi da kisan 'yar jarida a Abuja

Farashin fetur zai ci gaba da sauka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, ya ce farashin man fetur zai ci gaba da saukowa har zuwa karshen 2025.

Bismarck Rewane ya yi magana ne bayan Dangote da NNPCL sun rage farashin fetur, wanda hakan zai rage radadin wahala ga ’yan Najeriya.

Masanin tattalin arzikin ya kuma bayyana cewa gogayya da ake yi a kasuwa tsakanin Dangote da NNPCL za ta amfanar da masu sayen fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com