Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 25 a Kano

Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 25 a Kano

-Hukumar kula da lamurran gidajen man fetur ta DPR ta rufe gidajen mai 25 a jahar Kano

-Jagoran hukumar mai kula da jihohin Kano da Jigawa ne ya sanar da wannan labari ga manema labarai a ranar Alhamis

-A cewarsa aikin nasu ya kunshi binciken gidajen mai 217 ne inda aka samu 25 daga cikinsu sun saba dokokin hukumar DPR kana aka rufesu nan take

Hukumar kula da gidajen man fetur ta Najeriya wato DPR ta rufe gidajen mai 25 a jihar Kano. Jagoran hukumar mai kula da jihohin Kano da Jigawa ne ya bada wannan sanarwa ranar Alhamis inda ya ce, hukumar ta gudanar binciken gidajen mai 217 inda aka samu 25 da laifuka.

Jagoran mai suna Musa Tambawal ya shaidawa manemna labarai cewa gidaje man da aka rufe an same su ne da laifin bayar da mai ba bisa ka’ida ba, rashin lasisin sayar da man da sauran wasu laifuka da dama.

KU KARANTA:Wani mutum ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa saboda ta hanashi saduwa da ita

Tambawal ya bayyana mamakinsa a fili kasancewar akasarin gidajen man da aka garkame na ikirarin cewa ba su da masaniya a kan dokokin hukumar ta DPR. Amma ya tattbatar masu cewa za’a hukunta dukkanin gidajen man da aka samu da laifi.

Ya sake yin gargadi ga masu kasuwancin man fetur da su guji yin duk wani abinda suka tabbata cewa ya sabawa doka saboda akwai hukunci na musamman da aka tanada ga masu yin hakan.

A karshe, ya umarci gidajen man da aka rufe da su tafi zuwa yin sabon lasisin sayar da man fetur domin gudun abinda kan iya biyo baya nan gaba kadan.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ne ya kawo mana wannan labarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel