Mansur Sokoto Ya Yi Gugar Zana da Tinubu Ya Yafe wa Masu Kisa da Safarar Kwaya
- Fitaccen Malamin Hadisi, Farfesa Mansur Sakkwato ya bayyana abin da Allah SWT Ya yi umarni a kan wadand ke ketare iyakokin da Ya gindaya
- Ya bayyana haka ne bayan ya yi ce babu wani 'dan adam ya ke da iko ko hurumin ya yafe laifuffukan da wadansu su ka aikata na shiga hakkin wasu
- Farfesa Mansu ya fadi haka ne bayan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da yafe wa wadanda su ka aikata mugayen laifuffuka a kasar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sakkwato – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Ibrahim Sakkwato, fitar da wani sako mai kama da hannunka mai sanda bayan afuwar Bola Tinubu.
A tsakiyar makon nan ne Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da yafe wa wadansu masu laifi da ke garkame a gidajen kurkuku, daga cikinsu akwai wadanda su ka yi kisan kai.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Farfesa Mansur ya bayyana cewa babu wani mutum da ke da ikon yafewa wanda ya ketara umarnin da Allah SWT Ya shimfiɗa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu: Farfesa Mansur ya magantu kan yafe laifi
A cikin wani rubutu da Farfesan ya wallafa, ya bayyana cewa laifi, musamman wanda ya shafi hakkin wani ba ya daga cikin hurumin da wani 'dan adam zai tsoma baki a kai.
Ya yi ishara da maganar Annabi Muhammad (S.A.W.) wanda ya ce:
“Na rantse da Allah, da Fatima ‘yar Muhammadu ta yi sata da na yanke mata hannu.” (Bukhari 3475, Muslim 1688).
Ya ce wannan hadisin yana nuna adalcin da Musulunci ya gina tsarin rayuwa a kai — cewa hukunci na Allah ba ya nuna bambanci tsakanin mai ƙarfi da mara ƙarfi, ko talaka da mai mulki.
Farfesa Mansur: Yafe wa wani tsallake iyaka ne
Farfesa Mansur ya jaddada cewa duk wanda ya yi yunkurin yafe laifin da wani 'dan adam ya aikata, kuma aka tabbatar ya yi, wannan zalunci ne da tsallake iyakokin Allah SWT.

Source: Facebook
Ya ambaci ayar Alƙur’ani inda Allah Madaukakin Sarki Ya ce:
“Kuma duk wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne azzalumai.” (Suratul Baƙara: 229).
Farfesan ya yi nuni da cewa, mutum ba zai iya tserewa daga hukuncin Allah SWT gaba ɗaya ba, domin duk wanda ya guje wa wani hukunci, to zai fuskanci wani daban a rayuwarsa.
Ya ce wannan yana zama darasi ga al’umma cewa ingantaccen zaman lafiya ba zai tabbata ba sai an koma ga dokokin Allah SWT.
Tinubu ya yafe wa wasu 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince yin afuwa ga wasu daga cikin 'yan Najeriya da kotu ta tabbatar masu da laifuffukan da ake zargin sun aikata.
Shugaban Kasa ya amince da yafe wa mutane 175, wadanda wasu daga cikinsu na raye, wasu kuma an riga an aiwatar masu da hukuncin kisa bisa laifuffukan da su ka yi.
Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwa akwai Herbert Macaulay, fitaccen dan kishin ƙasa da Mamman Vatsa, tsohon ministan birnin tarayya, da aka kashe kan zargin yunkurin juyin mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


