Babbar Magana: An Kama Fasinjojin Jirgin Sama da Tsabar Kudi Kusan Naira Biliyan 10

Babbar Magana: An Kama Fasinjojin Jirgin Sama da Tsabar Kudi Kusan Naira Biliyan 10

  • Wasu fasinjoji sun shiga hannun jami'an tsaron filin jirgin sama a jihar Legas bayan kama su da tsabar kudi sama da Dalar Amurka miliyan 6.1
  • Rahotanni sun nuna an kama wadanda ake zargin ne a sashen harkokin sufurin cikin gida a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas
  • Tuni dai jami'ai suka mika su ga hukumar EFCC domin ci gaba da bincike amma wasu majiyoyi sun ce ana zargin kudin na wani dan siyasa ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Jami’an tsaro da ke aiki a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas sun kama wasu fasinjoji dauke da makudan kudi, suna shirin hawa jirgi zuwa wani wuri.

Rahotanni sun nuna cewa an kama fasinjojin da tsabar kudi har Dalar Amurka sama da miliyan 6.1, kusan Naira biliyan 10 kenan a kudin gida Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Filin jirgin sama na Murtala Muhammad.
Hoton harabar filin jirgin Murtaba Muhammad da ke jihar Legas. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kama fasinjojin jirgin Legas da tsabar kudi

Majiyoyi da ke da masaniya game da lamarin, wadanda suka bukaci a boye sunayensu saboda ba su da ikon magana da 'yan jarida, sun tabbatar da hakan ga Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai daga majiyoyin sun nuna cewa an kama fasinjoji da wadannan kudi masu nauyi ne yayin da suke shirin hawa jirgin sama na kamfanin Aero Contractors a filin jirgin Murtala Muhammed.

Bugu da kari, an tattaro cewa ana zargin matasan da aka kama suna dauke da kuɗin ne a madadin wani babban mutum da ake kyautata zaton yana da mukamin siyasa.

Duk da har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin amma majiyoyin sun ce jami’an Aviation Security (AVSEC) ne suka kama mutanen a MMA 1, sashen tashar jirgin cikin gida.

Jami'an AVSEC sun mika su ga hukumar EFCC

An ruwaito cewa bayan an kama su, jami'an sun mika su hannun jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) domin ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Sokoto

Wani babban jami’in AVSEC ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:

"Har yanzu muna aiki tare da hukumar EFCC domin gano cikakken bayani game da wannan kuɗi.”
Jami'an hukumar EFCC.
Hoton jami'an hukumar EFCC a bakin aiki. Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Da aka tuntubi mai magana da yawun Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Faithful Hope-Ivbaze, ta nemi a turo tambayar ta sakon salula.

Kuma duk da an aika mata da sakon, har zuwa lokacin da mume hada wannan rahoto ba ta turo amsa ba, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

A halin yanzu dai ana dakon jin cikakken bayani a hukumance daga hujumar EFCC ko mahukuntar filayen jirgin sama kan mutanen da aka kama da wadannan kudi.

Jirgin sama ya yi gaggawar komawa Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wata fasinja mace ta shiga mawuyacin rashin lafiya a cikin jirgin Ibom Air bayan ya tashi daga Abuja zuwa Legas.

Ma’aikatan jirgin sun gaggauta bai wa matar taimakon farko ganin yadda rashin lafiyarta ta tsananta jim kadan bayan tashin jirgin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi

Rahotanni sun tabbatar da cewa likitocin sun yi nasarar dawo da numfashi da bugun zuciyar matar kuma yanayinta ya daidaita bayan jirgin ya koma Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262