Saudiyya Ta Gindaya Sharudda Masu Tsauri ga Musulman da Za Su Tafi Aikin Hajjin 2026

Saudiyya Ta Gindaya Sharudda Masu Tsauri ga Musulman da Za Su Tafi Aikin Hajjin 2026

  • Kasar Saudiyya ta ja hankalin kasashen musulmi game da ka'idojin lafiya yayin da ake shirye-shiryen aikin Hajjin 2026
  • Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta fitar da ka'idoji da sharuddan lafiya da take bukatar kowane mahajjaci ya kiyaye tun kafin ya baro kasarsa
  • Tuni dai Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta shawarci maniyyata su cika duka sharuddan da Saudiyya ta gindaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudiyya - Hukumomin Saudiyya ta fitar da sababbin sharuddan kiwon lafiya ga mahajjatan da ke shirin gudanar da aikin Hajji na shekara ta 2026 (1447 Hijira).

Sharuddan da hukumomin Saudiyya suka fitar sun haɗa da wadanda dole ne musulmin da ke shirin zuwa sauke farali ya bi su kafin tafiya zuwa ƙasa mai tsarki.

Saudiyya.
Hoton masallaci harami cike da mahajjata a kasar Saudiyya. Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta ce duka kasashe, ciki har da Najeriya, su ke da alhakin tabbatar da cewa mahajjatansu suna cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

APGA: Yadda tsoron EFCC ke kora gwamnoni, 'yan adawa zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saudiyya ta gitar da ka'idojin lafiya

Haka zalika, ta bukaci hukumomin alhazai na kasashe su tabbata cewa mahajjatansu ba su dauke da cututtuka da ka iya barazana ga kansu ko wasu yayin ibada.

Daga cikin cututtukan da za su iya hana mutum shiga Saudiyya akwai matsanancin ciwon zuciya, huhu, koda ko hanta da cututtuka masu tsanani da suka dade.

Sauran lalurorin da Saudiyya ta jero sun hada da tabin hankali ko rashin nutsuwa; juna biyu; masu jinyar ciwon daji; da kuma masu dauke da cututtuka masu yaduwa kamar tarin fuka da zazzabin jini.

Abubuwan da ake bukata daga mahajjata

Kowane maniyyaci zai gabatar da takardar shaidar lafiya daga ƙasarsa, wadda ke tabbatar da cewa ba shi da wata daga cikin wadannan matsalolin.

Haka kuma, takardar rigakafi za ta zama wajibi, domin tabbatar da cewa mahajjata sun karɓi allurar rigakafi da ake buƙata kafin shiga Saudiyya.

Za a gudanar da binciken lafiya a dukkan filayen jiragen sama da iyakokin ƙasar. Duk wanda bai cika sharuddan lafiya ba, za a iya hana shi shiga, killace shi, ko kuma zurfafa bincike.

Kara karanta wannan

ADC ta yi kaca kaca da Tinubu kan yafe wa masu safarar miyagun kwayoyi

Ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya ta jaddada cewa ba za a bari duk wani mahajjaci da ke fama da wadannan cututtuka ya shiga ƙasar ba, kuma za a binciki takardun lafiya a tsanaki.

Haka kuma, Saudiyya ta ce za ta iya ƙara wasu matakai idan aka samu barkewar cuta ta duniya tare da haɗin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Maniyyata a wurin aikin Hajji.
Hoton alhazai a dutsen arafah yayin aikin hajjin shekarar 2025. Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

A Najeriya, Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta shawarci masu niyyar zuwa Hajji su fara cika wadannan sharuddan lafiya da rigakafi tun da wuri don guje wa matsalolin shiga Saudiyya.

Tinubu ya umarci a rage kudin Hajjin 2026

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin rage kudin kowace kujerar Hajjin badi ta shekarar 2026 ga musulman Najeriya.

Yayin wannan ganawa a fadar shugaban kasa, Tinubu ya umarci NAHCON ra rage kudin kujerar Hajji mai zuwa duba da yadda farashin Naira ke farfadowa.

Ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce saukaka wa maniyyata kudin da za su biya, la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262