An Jero Sunayen Tsofaffin Gwamnoni 2 da Ka Iya Maye Gurbin Minista a Gwamnatin Tinubu

An Jero Sunayen Tsofaffin Gwamnoni 2 da Ka Iya Maye Gurbin Minista a Gwamnatin Tinubu

  • Ministan kimiyya da fasaha a Najeriya ya yi murabus saboda zargin gabatar da takardun bogi ga majalisar tarayya yayin tantance shi
  • Murabus din Uche Nnaji, ya bude kofa ga nadin sabon minista daga Jihar Enugu, inda ake shirin fafatawa tsakanin tsofaffin gwamnoni biyu
  • Masana siyasa sun ce Dr. Davidson Nnamani na da damar samun nasara, ganin shekarunsa da kwarewarsa a fannin dabarun tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu - Biyo bayan murabus din tsohon Ministan Kimiyya, Kirkire-Kirkire da Fasaha, Cif Uche Nnaji, an fara hasashen masu maye gurbinsa ba tare da bata lokaci ba.

Kofa ta bude a gurbin sabon minista daga Jihar Enugu da ke Kudu maso Gabas wanda aka fara hasashen mutane uku za su iya samu.

Ana hasashen wadanda za su maye gurbin minista da ya yi murabus
Shugaba Bola Tinubu da tsohon minista, Uche Nnajo. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

An fara hasashen masu maye gurbin kujerar minista

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a jihar Benue, an yi asarar rayuka kafin zuwan sojoji

Rahoton Vanguard ya ce wannan ya haifar da fafatawa tsakanin tsofaffin gwamnoni biyu daga jihar, Sullivan Chime da Ifeanyi Ugwuanyi.

Har ila yau, daga cikin wadanda ake hasashen akwai kuma masanin tsaro, Dr. Davidson Nnamani daga jihar wanda matashi ne da wasu ke ganin zai fi dacewa da mukamin.

Rahotanni sun nuna cewa Chime da Nnamani ‘yan jam’iyyar APC ne, yayin da Ugwuanyi na jam’iyyar PDP kuma yana daga cikin kungiyar G-5 da ke goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.

Masana siyasa sun bayyana cewa Dr. Nnamani, wanda matashi ne kuma masanin tsaro, yana da damar zama sabon ministan saboda gogewarsa da hangen nesansa.

Wani abu da ke tasiri a wannan zaben shi ne tsarin raba mukamai tsakanin yankin Enugu da kuma bangaren Nsukka.

Wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni da ake hasashen za su zama ministoci
Tsofaffin gwamnonin Enugu, Sullivan Chime da Ifeanyi Ugwuanyi. Hoto: Sullivan I Chime, Hon. Ifeanyi Ugwuanyi.
Source: Facebook

Yadda zaben sabon minista zai iya jawo rigima

Duk ministocin baya sun fito daga Enugu, alhali yankin Nsukka, wanda ke da fiye da rabin masu kada kuri’a, bai taba samar da minista ba tun shekarar 1999 da aka dawo mulkin dimukradiyya.

Wasu majiyoyi suka ce tsohon Gwamna Sullivan Chime daga karamar hukumar Udi yana yin bin kafa a sirrance, yayin da Ifeanyi Ugwuanyi daga Udenu ya dogara da alakar da yake da shi da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Dalilin da ya sa ministan Tinuhu ya yi murabus

A gefe guda, Dr. Davidson Nnamani daga Isi-Uzo yana da digiri na uku a fannin dabarun tsaro daga babbar makarantar sojoji ta NDA, kuma ana ganin shi mutum ne mai kishin kasa da tunani mai zurfi.

A karshe dai, shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai yanke shawarar wanda zai wakilci Jihar Enugu a Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC).

Dalilin murabus din minista, Uche Nnaji

Mun ba ku labarin cewa bayanai sun fito kan dalilin murabus din tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji bayan zargin amfani da takardun bogi na digiri da na NYSC.

An ce wasu hadiman shugaban kasa sun bayyana cewa Bola Tinubu ne ya kira Nnaji zuwa fadar shugaban kasa, inda ya umurce shi da ya yi murabus.

Hakan ya biyo bayan wani bincike kan takardun ministan da aka ce ya gabatar da na bogi ga Bola Tinubu da kuma majalisar tarayya yayin tantance shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.