An Fara Guna Guni da Majalisar Benue Ta Amince Gwamna Ya Karbo Bashin Naira Biliyan 100

An Fara Guna Guni da Majalisar Benue Ta Amince Gwamna Ya Karbo Bashin Naira Biliyan 100

  • Jam'iyyar PDP ta soki shirin Gwamna Hyacinth Alia na karbo rancen Naira biliyan 100, ta ce hakan yunkuri ne na gurgunta jihar
  • Majalisar Dokokin Jihar Benuwai ta amince wa gwamnan ya ciyo wannan bashi bayan ya gabatar da ayyukan da zai yi wa al'umma
  • Gwamna Alia ya ce zai yi amfani da kudin wajen gudanar da ayyukan more rayuwa da za su taimaki mutanen jihar Benuwai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Majalisar Dokokin Jihar Benuwai, a ranar Jumma’a ta amince da bukatar Gwamna Hyacinth Alia ta karɓo rancen Naira biliyan 100.

Gwamna Alia ya gabatar da bukatar ciyo bashin ga Majalisar ne domin gudanar da wasu ayyukan more rayuwa da za su inganta rayuwar al'umma.

Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia.
Hoton gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia a gidan gwamnati. Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Source: Facebook

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa Majalisar Dokoki ta amince da bukatar gwamna ne a wani zaman gaggawa da Kakakin majalisar, Alfred Emberga, ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Ya bar PDP? Gaskiya ta fito game da 'sauya sheƙar' tsohon gwamnan Benue zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu ayyuka Gwamna Alia zai yi da N100bn?

A cikin wasikar da Kakakin ya karanta wa ‘yan majalisa, Gwamna Alia ya bayyana cewa rancen zai taimaka wajen gyara da samar da kayan aiki a asibitoci 23 na gwamnati.

Haka kuma za a yi amfani da kudin wajen gina sababbi da gyaran makarantu na kimiyya, kammala aikin hanyoyi da gadaje, gina cibiyoyin koyon sana’o’i, da kafa makarantu na zamani a kowace mazabar tarayya ta jihar Benue.

Haka kuma, kudin za su taimaka wajen ginawa da samar da kayan aiki ga Jami’ar Noma, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Benue da ke Ihugh, tare da wasu muhimman ayyuka.

Majalisa ta amince gwamna ya karbo bashi

Majalisar ta amince da bukatar gwamnan gaba ɗaya, amma ta yi kira ga gwamnatin jihar ta yi amfani da kuɗin cikin gaskiya da adalci domin ci gaban jama’a da Benue baki ɗaya.

Sai dai, jam’iyyar adawa ta PDP a jihar ta soki wannan mataki, tana cewa “babu lissafi a cikin rancen kuma bai dace da halin tattalin arzikin da jama’a ke ciki ba.”

Kara karanta wannan

Majalisa ta cin ma matsaya kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na jihar, Tim Nyor, ya sanya wa hannu.

PDP ta soki shirin Gwamna Alia

Jam’iyyar PDP ta yi ikirarin cewa babu gaskiya a shirin karbo bashin N100bn da Gwamna Alia ke yi domin akwai abubuwan da ake boye wa.

Bugu da kari, PDP tai zargin cewa ciyo bashi mai yawa haka zai iya jefa jihar Benue cikin sabon nauyin bashi da ba za a iya biya ba, in ji rahoton Daily Post.

Tutar PDP.
Hoton tutar jam'iyyar adawa ta PDP. Hoto: OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta kuma bukaci majalisar dokokin Benuwai da ta sake tunani kan wannan mataki, tana cewa:

“Ya kamata majalisar ta yi aikinta cikin tsari da daidaito, ba wai ta zama yar amshin shata ba."

Gwamna Alia ya dakatar da ciyaman

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia ya dakatar da shugaban karamar hukumar Otukpo, da wasu manyan jami'an gwamnati biyu.

Tun farko, Majalisar dokokin jihar Benuwai ce ta ba Gwamna Hyacinth Alia shawarar dakatar da jami'an gwamnatin uku bayan binciken da ta yi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gwangwaje 'yar kabilar Igbo da kyautar ban mamaki a Borno

Gwamna Alia ya sake jaddada kudirinsa wajen bin doka da oda, bin ka’ida, da kuma kiyaye tsarin raba madafun iko.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262