Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram a Borno

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram
  • Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato makudan kudaden fansa da suka karba a hannun bayin Allah
  • Jami'an tsaron sun kuma raunata 'yan ta'adda a yayin artabun da aka dauki dogon lokaci ana gudanarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke aikin yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan ta'addan Boko Haram a Borno.

Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram guda tara tare da kwato kuɗin fansa har N5m yayin wani sintiri a Magumeri da Gajiram, hedkwatar karamar hukumar Nganzai a jihar Borno.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar OPHK, Laftanar Sani Uba, ya fitar a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

Laftanar Sani Uba ya bayyana cewa dakarun OPHK sun gudanar da wani sintiri a ranar 10 ga Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ‘yan Boko Haram a kusa da Goni Dunari da ke karamar hukumar Magumeri.

"Yan ta’addan da ke tafiya cikin motoci biyu da mutane 24 a kafa sun fara kona gidaje da tsoratar da mazauna yankin, wanda hakan ya sa sojojinmu suka yi gaggawar kai farmaki domin dakile barazanar."

- Laftanar Sani Uba

Ya ce yayin da sojojin ke kokarin isa wajen, ‘yan ta’addan sun yi yunkurin guduwa zuwa Damjiyakiri, inda waɗanda ke cikin motoci suka watse, yayin da sojojin suka bi sawun masu tafiya a kafa tsawon kilomita 92.

Bayan awanni huɗu na bin sawu, sojojin sun samu damar yin arangama kai tsaye da ‘yan ta’addan, inda suka kashe guda biyar, yayin da sauran suka tsere da raunuka, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun faki ido, sun kai hari sansanin sojojin Najeriya, an rasa rayuka da dama

"Ba a sami asarar rai ko kayan aiki daga bangaren sojojinmu ba a yayin wannan farmakin."

- Laftanar Sani Uba

Dakarun Sojoji sun kwato kudin fansa

Hakazalika ya bayyana cewa sojojin da ke sintiri a hanyar Gajiram – Bolori – Mile 40 – Gajiganna sun yi artabu da ‘yan Boko Haram a kusa da kauyen Zundur, inda suka kashe ‘yan ta’adda hudu.

Sojojin sun kuma ceto mutane biyu, wato Modu Kinnami (mai shekara 55) da Bukar (mai shekara 57), dukkansu ‘yan karamar hukumar Guzamala, tare da buhu ɗaya mai ɗauke da Naira 750,000.

“Bincike ya nuna cewa ‘yan Boko Haram sun nemi kuɗin fansa N2m da wayoyi biyu sababbi na Tecno kafin su saki ɗan’uwan waɗanda aka sace."

- Laftanar Sani Uba

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojojin sun kuma kwato abubuwan da suka hada da mota mai launin shuɗi mai lamba GUB 327 XA, sababbin wayoyi biyu na Tecno, jarka mai ɗauke da lita 30 na man fetur da jimillar kuɗi N4,355,000.

Sojoji na kokari

Sulaiman Abubakar ya shaidawa Legit Hausa cewa dakarun sojojin Najeriya na kokari wajen yaki da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Sokoto

"Sojoji na matukar kokari wajen yaki da 'yan ta'adda a sassa daban-daban na Najeriya. Muna yaba musu sosai."
"Matsalar Boko Haram ta dade a kasar nan, muna rokon Allah ya ci gaba da ba sojojinmu nasara kan 'yan ta'adda."

- Sulaiman Abubakar

Sojoji sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan bindigan ne yayin wani artabu da ya gudana a kauyen Sabon Garin Kwargaba, cikin karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto.

An hallaka 'yan bindigan ne lokacin da sojojin suka kai daukin gaggawa bayan 'yan bindiga sun yi dirar mikiya a kauyen.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng