Sarkin Musulmi Ya Yi Muhimmin Kira ga Gwamnonin Arewa

Sarkin Musulmi Ya Yi Muhimmin Kira ga Gwamnonin Arewa

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya yi kira da babbar murya ga gwamnonin Arewa
  • Sarkin Musulmin ya bukaci gwamnonin Arewa kan su maida hankali wajen kawo ci gaban da zai amfani mutanen yankin
  • Ya yi nuni da cewa mutanen Arewa ne da kansu za su samo mafita ga tarin kalubalen da ya addabi yankin ba wasu daga waje ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya aika sako ga gwamnonin Arewa.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bukaci gwamnonin Arewa da su kara jajircewa wajen haɓaka ci gaban yankin ta hanyar tabbatar da cewa tarurrukan zuba jari suna haifar da sakamako kyau.

Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a wajen bude taron tattalin arzikin Bauchi.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane sako Sarkin Musulmi ya aika?

Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya jaddada muhimmancin gaskiya da sakamako mai ganuwa daga irin waɗannan taruka.

Ya bayyana cewa kalubalen Arewa na bukatar mafita daga cikin gida wacce shugabanni masu hangen nesa za su jagoranta.

“Muna taruwa, muna gabatar da jawabai masu dadi, muna gayyatar manyan ‘yan kasuwa, amma a karshe, me muke samu?"
“Babu wanda zai iya gina Arewarmu fiye da mu kanmu. Dole ne mu ɗauki alhakin makomar mu."

- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar

Sarkin Musulmi ya bada shawara

Sarkin Musulmin ya shawarci mambobin kungiyar gwamnonin Arewa da su duba sakamakon tarurrukan zuba jari na baya domin tantance tasirinsu a rayuwar jama’a.

“Ina kira ga gwamnoninmu su waiwayi abubuwan da aka cimma daga irin waɗannan tarurruka, mene ne ainihin canjin da suka kawo ga jama’armu?”

- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Ya yaba wa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, bisa shirya taron, yana mai jaddada cewa dole irin waɗannan tarurruka su zama matakin aiwatar da manufofi da za su inganta zaman lafiya, samar da ayyukan yi, da dorewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: Atiku ya nemi a binciki Tinubu da ministocinsa kan takardun bogi

“Za ka iya gayyatar masu zuba jari, amma idan babu tsaro, ba za su tsaya ba. Tsaro shi ne ginshiƙin kowane irin ci gaba."

- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar

Sarkin Musulmi ya shawarci gwamnonin Arewa
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar. Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Twitter

Haka kuma ya shawarci shugabanni a duk matakai da su yi mulki cikin adalci, gaskiya da tsoron Allah, yana mai cewa kyakkyawan shugabanci da rikon amana ne ginshikin samun yardar jama’a.

Ya kammala jawabinsa ta hanyar yin kira ga 'yan Najeriya kan hadin kai da kishin kasa, inda ya nuna cewa za a iya samun ci gaba ne kawai ta hanyar zaman lafiya.

"Ba mu da wata kasa wadda ta wuce Najeriya. Dole ne mu hadu tare wajen tabbatar da cewa ta samu ci gaba."

- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar

Sarkin Musulmi ya koka kan bangaren shari'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya koka kan matsalolin da ke faruwa a bangaren shari'a.

Sarkin Musulmin ya yi gargadin cewa adalci a Najeriya yana ruguje wa saboda yanzu masu kuɗi ne kawai ke iya sayen adalci a gaban alkalai.

Kara karanta wannan

Gidajen mutane da gonaki sun nutse cikin ruwa, ambaliya ta yi barna a Najeriya

An ji cewa ya bayyana hakan a lokacin da ya yi jawabi a taron shekara-shekara na ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) da aka gudanar a Enugu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng