Masu Digiri Dan Kotono Sun Kawo Dabarar Yaudara a Najeriya wajen Shiga NYSC

Masu Digiri Dan Kotono Sun Kawo Dabarar Yaudara a Najeriya wajen Shiga NYSC

  • Wasu jami’o’i a Jamhuriyar Benin da aka dakatar sun haɗa kai da kwalejojin Najeriya wajen shigar da ɗalibansu cikin hidimar NYSC
  • Ana ce wa ɗaliban suna biyan kusan N400,000 don samun takardar diflomar HND daga kwalejojin da ke wasu yankunan Najeriya
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami’o’in suna amfani da sunan kwalejoji masu zaman kansu domin ɓoye asalin takardun su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami’o’i da Najeriya ta soke a Jamhuriyar Benin suna amfani da wasu hanyoyi wajen saka ɗalibansu a shirin hidimar ƙasa (NYSC).

Wani rahoto ya yi zargin cewa masu digiri dan Kotono suna hakan ne ta hanyar haɗin gwiwa da wasu kwalejojin kimiyya da fasaha na Najeriya.

Masu hidimar kasa a Najerya
Wasu masu hidimar kasa (NYSC) suna fareti a Najeriya. Hoto: National Youth Service Corps
Source: Twitter

Binciken jaridar Punch ya gano cewa jami’o’in suna sayen takardun ND da HND daga waɗannan kwalejoji domin ɗalibansu su samu damar yin hidimar ƙasa.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin cewa ɗaliban suna biyan kuɗi masu tsoka har zuwa N400,000 don samun takardar HND da za ta basu damar shiga NYSC.

Jami’o’in Kotono da aka dakatar a Najeriya

A 2024 ne gwamnatin tarayya ta dakatar da takardun karatu daga jami’o’in Jamhuriyar Benin da Togo bayan rahoton da ya fallasa cuwa-cuwa a fannin bayar da digiri cikin makonni kaɗan.

Rahoton ya nuna cewa ɗalibi na iya samun takardar digiri daga jami’a a Kotono cikin mako shida kacal, sannan ya shiga NYSC a Najeriya.

Bayan wannan, jami’o’in da abin ya shafa suka koma neman mafita ta hanyar yin haɗin gwiwa da kwalejojin Najeriya domin ci gaba da shigar da ɗalibansu cikin NYSC.

Hanyar da ake bi wajen yaudarar gwamnati

Wani ɗalibi daga jami’ar Esfam-Benin da ke Porto Novo, mai suna Seun, ya bayyana cewa an tura bayanan karatunsa zuwa wata kwalejoji ta Najeriya domin sarrafa takardunsa.

Kara karanta wannan

Cikakken sunayen kasashe 7 da suka sassauta matakan ba da biza ga 'yan Najeriya

Ya ce wasu abokansa ma sun riga sun karɓi takardun HND kuma suna jiran a tura su NYSC kafin ƙarshen shekara.

Seun ya bayyana cewa:

“Idan mutum yana da kuɗi, zai iya samun takardar digiri daga Benin sannan ya sake biyan kuɗi domin samun sabuwar takarda daga kwalejin Najeriya wadda ke ba shi damar yin hidimar ƙasa.”

Karin bayani daga wasu dalibai

Wani ɗalibi daga wata jami’a da aka haramta a Benin ya tabbatar da cewa wani jami’in makarantar su ne ya tsara wannan hanyar bayan gwamnati ta soke takardunsu.

Ya ce jami’in ya ce su biya wani adadi domin su samu takardar HND daga kwalejin Najeriya, sannan su yi rajista da JAMB domin su shiga jerin sunayen ɗaliban da za su yi NYSC.

Wani ɗalibi daga Abia ya kuma bayyana cewa ya samu takardun ND da HND daga wata kwaleji kuma yana jiran shiga NYSC kafin ƙarshen shekara.

Ministan ilimi, Dr Alausa
Ministan ilimin Najeriya, Dr Tunji Alausa na jawabi. Hoto: Federal Ministry of Education
Source: Facebook

Yadda ake hada takardun bogin

Wani jami’i daga jami’ar Porto Novo wanda ya taɓa shiga cikin makircin ya bayyana cewa an daina aikin bayan gwamnati ta fara bincike.

Kara karanta wannan

Abin da Mahmood Yakubu ya fadawa Tinubu a takardar ajiye shugabancin INEC

Ya bayyana cewa jami’o’in Benin suna aika da bayanan ɗalibai zuwa kwalejojin Najeriya, waɗanda su kuma ke saka sunayen ɗaliban a jerin masu shiga cikin tsarin NYSC.

Ya ƙara da cewa ɗaliban na biyan kuɗi kafin a fara aikin, sannan kwalejojin su ne ke ƙirƙirar sabuwar takarda mai ɗauke da sunayen su a matsayin ɗalibansu.

Rahotanni sun nuna cewa tsarin ya fi yawa a Kudu maso gabas da Kudu maso Yamma, inda jami’o’in Benin ke amfani da kwalejojin Najeriya wajen badakala.

Jami'o'i mafi nagarta a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa an fitar da jerin jami'o'i mafi nagarta a duniya da kuma Najeriya a shekara mai zuwa.

Rahotanni sun nuna cewa jami'ar Ibadan ce ta zamo farko a fadin Najeriya yayin da jami'ar Legas ke binta a baya.

A daya bangaren kuma, jami'ar Bayero da ke Kano ce ta zo ta uku yayin da jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta zo ta shida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng