Batanci: Bala Lau Ya Goyi bayan Triumph, Ya Yi Kira ga Mataimakin Gwamnan Kano

Batanci: Bala Lau Ya Goyi bayan Triumph, Ya Yi Kira ga Mataimakin Gwamnan Kano

  • Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa Ahlussunnah ne ke kare martabar Manzon Allah (S.A.W) tare da bin koyarwar Alƙur’ani da Hadisai
  • Malamin ya ce Sheikh Triumph yana faɗakar da Musulmai kan haɗarin jingina abubuwan da ba su da hujja ga Manzon Allah (S.A.W)
  • Shugaban JIBWIS ya gargadi gwamnati da kada ta tsoma siyasa cikin binciken da ake yi kan muhawarar Triumph da wasu malamai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Sheikh Lawal Abubakar Shu’aib Triumph a sabanin da aka samu a Kano.

Sheikh Bala Lau ya bayyana hakan ne a yayin hudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin JIBWIS na ƙasa da ke unguwar Utako, Abuja, a ranar 10, Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

A sakon da shafin Jibwis ya wallafa a Facebook, Bala Lau ya jaddada cewa Ahlussunnah ne masu tsayawa wajen kare martabar Manzon Allah (S.A.W).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan muhawara darasi ce ga al’umma domin ta gane bambanci tsakanin gaskiya da abin da wasu ke jingina wa addini ba tare da hujja ba.

Maganagu kan girmama Annabi Muhammad SAW

Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa Ahlussunnah ne ke kare gaskiya da tsarkake da’awar Musulunci daga abubuwan da ba su da tushe a cikin Alƙur’ani da Hadisai.

Ya ce da’awar Ahlussunnah tana gudana bisa tafarkin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya shimfiɗa, kuma duk wanda ke son Manzon Allah dole ne ya bi shari’a, ba ta hanyar jahilci ba.

Shehin malamin ya jaddada cewa sahabbai ne suka fi kowa sanin matsayin Annabi, kuma su ne suka fi nuna soyayya gare shi cikin natsuwa da ilimi.

Bala Lau: 'Triumph na kare addini da hujja'

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yabi CBN da Tinubu, ya kawo hujjojin fitowa daga kangin tattalin arzik

Da yake tsokaci kan lamarin da ya shafi Sheikh Triumph, Bala Lau ya ce malamin yana ƙoƙarin gyara fahimtar Musulmi kan yadda wasu ke jingina karamomi ga shehunnan su.

Ya bayyana cewa Triumph yana nufin al’umma su gane cewa soyayya ga Annabi tana tabbata ne da ilimi da hujja, ba da jahilci ba.

Sheikh Bala Lau ya ce irin wannar da’awa tana taimakawa wajen kare Musulunci daga ɓatanci da kuma ƙarfafa bin ingantattun koyarwar addini.

Sheikh Lawan Triumph Kano
Sheikh Triumph yana gabatar da wa'azi a Kano. Hoto: Sheikh Lawan Abubakar Shuaibu Triumph
Source: Facebook

Gargaɗin kada gwamnati ta tsoma siyasa

Shugaban JIBWIS ya gargadi gwamnatin jihar Kano da kada ta tsoma siyasa cikin binciken da ake yi kan rikicin Triumph da wasu malamai.

Ya ce kamata ya yi a bari hujjojin Alƙur’ani da Hadisai su zama ginshiƙi wajen tantance gaskiya, ba son rai ko matsin lamba ba.

A ƙarshe, Sheikh Bala Lau ya ce akwai siyasa a furucin mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya ce kama Abduljabbar Nasiru Kabara lamari ne na siyasa.

Ya bayyana cewa kama Abduljabbar ya samo asali ne daga haɗin kai tsakanin Malaman Izala, Tijjaniya da sauran kungiyoyin Sufaye, saboda koyarwarsa ta sabawa Alƙur’ani da Hadisai.

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Triumph: Maganar Gumi kan rikicin Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan sabanin da aka samu a Kano da Malam Lawan Triumph.

Gumi ya bukaci gwamnatin jihar ta fahimci cewa hayaniya ce da za ta iya kawar da hankalin al'umma.

Malamin ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta dauki salon daukar nauyin saka karatun addini a kafafen sadarwa domin fahimtar da mutane gaskiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng