Ana Barazanar za a Hallaka Ministan Tinubu, Ya Kara Yawan Jami'an da Ke Tsaronsa

Ana Barazanar za a Hallaka Ministan Tinubu, Ya Kara Yawan Jami'an da Ke Tsaronsa

  • Dele Alake ya nunka jami'an tsaronsa sau uku bayan samu barazanar kisa daga wadanda aka soke wa lasisin hakar ma’adinai
  • Ministan ya ce har a wayarsa ana aika masa da sakonnin barazana, inda wasu ke ƙoƙarin tilasta gwamnati ta sauya matakanta
  • Ana yi wa ministan barazana ne bayan da gwamnati ta soke fiye da lasisi 3,700 na mutane da kamfanonin da ke hakar ma'adanai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Ministan bunkasa harkokin ma’adinai na tarayya, Dele Alake, ya bayyana cewa ya ninka yawan jami’an tsaronsa sau uku.

Dele Alake ya dauki matakin ne bayan samun barazanar kisa da dama daga wasu mutane da kamfanoni da aka soke musu lasisin hakar ma’adinai.

Minista kara yawan masu tsaronsa bayan da ya samu sakonnin barazana ga rayuwarsa
Shugaba Bola Tinubu ya na sauraron jawabi daga ministan ma'adanai, Dele Alake. Hoto: @AlakeDele
Source: Twitter

Ana barazanar hallaka ministan Tinubu

Ministan ma'adanan ya ce barazanar da ake yi masa ta haɗa da saƙonnin rubutu kai tsaye zuwa wayarsa, kamar yadda rahoton Leadership ya nuna.

Kara karanta wannan

"Tsohon shugaban kasa ya yi karya," Sanata Kalu ya tona abin da ya faru a kafin zaben 2007

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele Alake ya bayyana cewa yawan barazanar kisa da yake samu ya karu sosai har sai da ya yanke shawarar ƙara jami’an tsaro da ke gadinsa.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai, a shirin makon ma'aikatar ma'adai karo na 10, wanda zai gudana daga 13 zuwa 15 ga Oktoba, 2025, a Abuja.

Taken taron na wannan lokaci shi ne: “Hakar ma'adanai a Najeriya: Daga ci gaba zuwa goga kafada da kasashen duniya," kuma zai haɗa ’yan kasuwa, masu saka jari da masu tsara manufofi don tattauna wa kan cigaban fannin ma’adinai.

“Na samu barazanar kisa a wayata” – Minista

A cewarsa, ƙoƙarinsa na tilasta bin doka da soke lasisin da ba a amfani da su ya fusata wasu manyan mutane da kamfanoni da suka dade suna cin gajiyar rashin bin ƙa’ida.

“Gaskiya na ninka tsarona sau uku. Na samu barazanar kisa kai tsaye daga waɗanda aka soke musu lasisi saboda saba wa dokoki. Wani ma ya turo min saƙo ta waya ta, yana yin barazana ga rayuwata."

Kara karanta wannan

Yadda wani 'dan Nijar yake yaudarar mata ya karbi kudi daga hotunan tsiraicinsu

- Ministan ma'adanai, Dele Alake.

Ya ce wasu daga cikin masu korafin sun fara yin barazana, yaɗa farfaganda a kafafen yada labarai da kuma ƙulla shirin bata suna, domin tilasta ma’aikatar ta sauya matsayinta.

Ya ce"

“Na ce fada masu su binciki tarihinmu — ba da wasa muka shiga wannan aiki ba. Mun yi gwagwarmaya har muka kai ga wannan matsayi, kuma ba za mu ja da baya ba."
An yi wa ministan barazanar kisa ne bayan kwace lasisin masu hakar ma'adanai 3,794.
Ministan ma'adanai, Dele Alake yana jawabi a zauren taro na ma'aikatar ma'adanai ta tarayya. Hoto: @AlakeDele
Source: Facebook

Minista ya soke lasisi fiye da 3,700

Rahoton jaridar Punch Online ya nuna cewa barazanar ta biyo bayan soke lasisi 3,794 na hakar ma’adinai da kuma ƙarin lasisi 1,263 da aka soke a cikin shekaru biyu da suka gabata ƙarƙashin jagorancin Dele Alake.

Sai dai ƙarin tsaro da ya yi ya saba da umarnin Shugaba Bola Tinubu, wanda ya takaita yawan jami’an tsaro ga ministoci da manyan jami’an gwamnati zuwa mutane biyar kawai, tare da motoci uku a jerin tawagar su don rage kashe kuɗi a gwamnati.

Kara karanta wannan

Bayan rage kudin Hajji, Tinubu ya ba malamin Musulunci kyautar babbar mota

Alake ya kuma zargi wasu kamfanoni da aka soke musu lasisi da yi wa gwamnati barazana da kuma zagon kasa, maimakon su cika sharuddan cikin gida da doka ta tanada.

'Dalilin nada ni ministan ma'adanai' - Alake

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dele Alake, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ba shi mukamin ministan ma'adanai ne saboda muhimmancin ma'aikatar.

Alake ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da ministoci 45 da Tinubu ya yi a ɗakin taron fadar shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa ma'aikatar bunƙasa ma'adinai ta ƙasa ma'aikata ce mai matuƙar muhimmanci a shirin da gwamnati take yi na sabunta tattalin arziƙin ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com