Auren Gata: Ma'aurata a Kano Sun Roƙi Gwamna Abba Alfarma domin Samun Dama
- Wasu maza magidanta a Kano sun nuna sha'awarsu kan shirin auren gata da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shirya domin rage gwauraye
- Ma'auratan sun roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haɗa su cikin shirin bikin auren da gwamnatin Kano ta shirya domin su iya ƙara mata
- Hukumar Hisbah ta tabbatar da cewa gwamnati na shirin auren ga kimanin mutane 2,000, kuma za a yi gwajin lafiya don inganta tarbiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirin gudanar da bikin auren gata ga mata da maza 2,000, wanda ya jawo hankalin wasu mazan aure.
Wasu mazan aure a jihar sun roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya ba su damar shiga shirin domin su ƙara aure kamar yadda addini ya halatta.

Source: Twitter
An tsara shirin da gwamnati ta dauki nauyi ne domin inganta tarbiyya, rage tsadar aure, da taimakawa matasa da zawarawa su samu aure cikin sauƙi, cewar rahoton Legit.ng.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hisbah ta fara shirin auren gata a Kano
Malam Mujahid Aminudeen, mataimakin kwamandan hukumar Hisbah, ya tabbatar da cewa ana shirye-shiryen gudanar da bikin tare da yin rajista da gwajin lafiya ga ma’aurata.
Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen rage aikata laifuffuka kamar karuwanci da shan miyagun ƙwayoyi tare da ƙarfafa zaman lafiya a cikin iyalai.
Mazan auren sun fara neman shiga shirin
Sai dai yanzu maza da ke da mata ɗaya sun ce wannan dama ce gare su don su ƙara aure ba tare da wahalar kuɗin lefe da kayan ɗaki ba.
Wani ɗan kasuwa mai suna Ahmed Sani ya ce ya shafe shekaru ashirin da aure kuma yana son ƙara aure amma tsadar bukukuwa na hana shi.
“Aure na biyu yana da lada, amma kuɗin lefe, kayan ɗaki, da kuɗin ɗaki suna da yawa, inda yake roƙon gwamnati ta taimaka."

Source: Facebook
Martanin wasu mazauna Kano
Haka ma wani ma’aikaci, Musa Bello, ya ce shigar da maza aure cikin shirin zai taimaka wajen hana aikata badala a boye da kuma kare mutuncin mata.
Ya bayyana cewa:
“Idan mutum na da iko amma tsadar aure ta hana shi, hakan na iya jefa shi cikin zina, wanda ya fi muni.”
Wani direban mota, Ibrahim Garba, ya ce matarsa ma ta karfafa masa gwiwa ya ƙara aure domin samun taimako a kula da gida da ‘ya’ya.
Ya ce sun shirya yin gwajin lafiya tare da matar da yake so, yana roƙon gwamnati ta haɗa su a cikin wannan shirin mai albarka.
Gwamna Abba Kabir ya shirya sake auren gata
Mun ba ku labarin cewa gwamnatin Kano ta fara shirin daurar da marayu da marasa aure a cikin tsarinta na auren gata da aka saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci a jihar.
A wannan karo na biyu da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke daukar nauyin auren, ta amince da Naira biliyan 1.6 domin tabbatar da komai ya tafi da kyau.
Daga cikin kudin, za a biya kudin lefe, kayan dakunan amarya da shirya bikin aure karkashin kulawar Ma'aikatar Harkokin Addini ta jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


