'Ba Aikin Mu ba ne,' Sanata Ya Fadi Masu Alhakin Tantance Takardun Ministoci

'Ba Aikin Mu ba ne,' Sanata Ya Fadi Masu Alhakin Tantance Takardun Ministoci

  • Majalisar dattawa ta warware rudanin da aka samu game da tantance wadanda shugaban kasa ke aika mata don nadin mukamai
  • Warware rudanin ya zo ne bayan bincike ya gano tsohon minista, Uche Nnaji ya yi amfani da takardun digiri da na NYSC na bogi
  • Sanata Ali Ndume ya ce ba aikin majalisa ba ne tantance wadanda za a ba mukamai, jami'an tsaro ne ke bincike kafin a kai masu sunaye

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar dattawa ta yi karin haske game da matakan da take bi wajen amince ko kin amince da nade-naden ministocin da ake gabatar mata.

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu ne ya yi karin hasken, matsayin martani game da badakalar tsohon minista, Uche Nnaji.

Sanata Ali Ndume ya kare majalisar dattawa game da tantance ministoci
Sanata Ali Ndume yana jawabi a zauren majalisar dattawa a Abuja. Hoto: @ChengerHabib
Source: Facebook

Badakalar takardun bogin Nnaji yana minista

Kara karanta wannan

NYSC: Jerin ministoci 6 da suka shiga badakalar takardun bogi a Najeriya

Idan ba a manta ba, jaridar Premium Times ta bankado cewa Nnaji, wanda yake rike da mukamin ministan kimiyya da fasaha, bai kammala karatun jami'a ba.

Binciken ya nuna cewa takardun digiri da na NYSC da ministan ya mikawa majalisar dattawa lokacin tantance shi na da ayar tambaya, da zargin na bogi ne.

Wannan bincike ya zurfafa, inda har jami'ar Najeriya (UNN) ta fito fili ta ce ministan bai kammala karatu ba, kuma ba ta ba shi takardar digiri ba.

Saboda wannan badakala da ta tashi, da kuma yadda kasar ta dauka, Uche Nnaji ya hakura da aikin, ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Tinubu.

Martanin majalisa kan tantance 'yan takara

Wannan lamari gaba dayansa ya jawo mutane na tambayoyi game da yadda majalisar dattawa ke tantance wadanda za a ba mukamai a gwamnatin tarayya.

Wasu na ganin, kamar majalisar ma ba ta yin aikinta yadda ya kamata, ma damar ba za ta iya gane cewa takardun mutum na bogi ne ko na gaskiya ba.

A wannan gabar ne, Sanata Ali Ndume, ya yi martani, yana mai cewa ba alhakin majalisa ba ne tantance wadanda za a ba mukami ba, aikin hukumar DSS ne.

Kara karanta wannan

Sallama da murabus: Jerin ministoci 9 da aka rasa a gwamnatin Bola Tinubu

A zantawarsa da Channels TV a ranar Alhamis, Sanata Ndume ya ce majalisa na tantance 'yan takara ne kawai bayan jami'an tsaro sun tantance su.

Ya ce hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce babbar hukumar da ke tantance masu hawa mukami, bayan gudanar da bincike kansu, sannan ta mika rahoton ga majalisa.

Sanata Ali Ndume ya kare majalisar dattawa game da tantance ministoci
Sanata Ali Ndume ya na jawabi ga manema labarai bayan wani taron jam'iyyar APC. Hoto: @asafaabdulwasi2
Source: Twitter

"Ba mu ke tantance wa, ku fahimta' - Sanata

Sanata Ali Ndume ya yi karin bayani da cewa:

"Tantancewa da kuma amincewa wasu abubuwa biyu ne. Kafin shugaban kasa ya turo da sunan wanda zai hau kujera ga majalisar dattawa, ana bi matakai, ciki har da binciken SSS. Hukumar SSS ce za ta fara tantance mutum tun da fari."

Sanata Ndume ya yi bayani cewa batun amfani da takardun bogi a Najeriya ya wuce duk tunanin mutane, kuma bai tsaya a kan 'yan siyasa kawai ba.

"Matsalar amfani da takardun bogi na da girman gaske a Najeriya," in ji Sanata Ali Ndume.

Ndume ya jaddada cewa majalisar dattawa na dogaro ne da rahotannin jami'an tsaro kafin daukar matakai kan wadanda shugaban kasa ya tura masu domin nadin mukamai.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da ake zargi da takardun bogi ya fadi dalilinsa na ajiye aiki

'Abin da ya sa na yi murabus' - Minista

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Geoffrey Nnaji, ya bayyana ainihin abin da ya jawo aya yi murabus daga mukaminsa.

Ya ce barin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi ba ya nufin ya amsa zargin da ake yi masa na amfani da takardun karatun bogi da aka yi zarginsa da shi.

Tsohon ministan ya yi wannan bayanin ne duk da cewa an samu hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa ya gabatar da takardun digiri da na NYSC na bogi ga gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com