Bayan Yafe wa Mutum 175, Tinubu Zai Bada Lambar Girmamawa ga Wasu kusan 1000
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta daura damara, za ta raba lambobin yabo da na girmama wa ga wasu kebantattun mutane a kasar nan
- Shugaba Tinubu dai ya amince da bai wa mutane 959 lambobin girmamawa saboda gudunmawar da su ka bayar a fannoni da dama
- Dr. Emanso Umobong, babbar sakatariya a Fadar Shugaban Kasa ce ta tabbatar da haka, ta kuma fadi lokacin da za a sanar da sunayen mutanen
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bai wa mutane 959 lambobin yabo na kasa da kuma lambobin girmama wa na musamman.
Mutanen da za su samu wadannan lambobi sun kunshi wadanda suka bada gudunmawa wajen cigaban Najeriya da walwalar dan Adam.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Dr. Emanso Umobong, babbar sakatariya a Fadar Shugaban Kasa, ya bayyana hakan ne bayan kammala taron Majalisar Koli a Abuja, a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu zai raba lambar yabo
Daily Trust ta wallafa cewa Umobong ta ce kwamitin lambobin girmamawa da Alkali Sidi Bage ke jagoranta ya fara aikin tantance wadanda za a karrama tun daga Agusta 2021.
Ta kara da cewa daga wancan lokaci zuwa yanzu, kwamitin ya tantance fiye da mutum 5,000, inda ya zabi mutane 824 don ba su lambobin yabo na kasa na 2024/2025.
Dr. Emanso Umobong, babbar sakatariya a Fadar Shugaban Kasa, ta kuma ce za a baiwa wasu 135 lambobin yabo na musamman.
Ta bayyana cewa lambobin girmamawa sun hada da wadanda suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar lafiya, wasanni, kafafen watsa labarai da kare muhalli.
Su wa Tinubu zai ba lambobin girmamawa?
Ta ce daga cikin wadanda Bola Tinubu zai karrama akwai Bill Gates don gudummawarsa a fannin kiwon lafiya da Uncle Sam Pemu saboda gudunmawarsa a aikin jarida.
Haka kuma za a baiwa Super Falcons da D’Tigress lambar yabo saboda nasarori a wasannin da su ka buga da kuma wasu 'yan Ogoni da su ka yi wa muhalli hidima.

Source: Facebook
Haka kuma za a karrama Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe ta INEC, don ayyukan da ya gudanar bisa tsarin dimokradiyya da bin doka da oda.
Dr. Emanso Umobong, ta tabbatar da cewa za a wallafa jerin sunayen wadanda suka samu lambobin girmamawa nan gaba kadan domin kowa ya gansu.
Tinubu ya yafe wa mutum 175
A wani labarin, mun wallafa cewa a zaman Majalisar Koli da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da yafiya ga 175 daga sassa daban-daban na Najeriya.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya gabatar da jerin sunayen masu neman afuwa a madadin shugaban kasa a babban birnin Abuja.
Daga cikin wadanda suka samu afuwa akwai Herbert Macaulay, sanannen ɗan kishin ƙasa, da Manjo Janar Mamman Vatsa (mai ritaya), tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


