Triumph: Sheikh Gumi Ya Kawo Mafita kan Rikicin Kano, Ya Yi Kira ga Abba Kabir
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci gwamnatin Kano da ta dauki matakin rufe hayaniyar addini da ke kara rura wutar rikicin
- Ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali kan tallafawa malamai wajen koyar da tafsirin Alkur’ani da fassarar Hadisai da Fiqhu
- Jawabin Gumi ya biyo bayan korafin da aka shigar kan Sheikh Lawan Shuaibu Triumph da kuma binciken da kwamitin Shura na jihar ya fara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta rufe hayaniyar addini da ke kara haifar da rudani tsakanin musulmai a jihar.
Ya fadi haka ne a karatun da ya gabatar ranar 9, Oktoba, 2025, inda ya ce gwamnati ta dauki hanyar da za ta kare mutuncin addini da kawar da rikicin da ke barazana ga zaman lafiya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan Sheikh Ahmad Gumi ne a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Gumi ya ce idan gwamnatin Kano tana son gaskiya da zaman lafiya, dole ta rufe wannan hayaniya da ke ta dada karuwa, ta kuma samar da hanyoyin ilmantar da jama’a.
Ahmad Gumi: 'Musulmai su guji rikici'
A cewarsa, Musulman Najeriya suna fuskantar barazana daga waje bayan yakin Gaza, inda wasu ke kokarin shigo da rikicin cikin kasar.
Saboda haka, ya shawarci Musulmai da su hada kai wajen kare martabar addininsu da gujewa duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kai.
Ya ce abin da ake bukata yanzu shi ne hadin kai da natsuwa. Kada a bari wasu su shigo da rikicin da zai karkatar da hankula daga abubuwan da suka fi muhimmanci.

Source: UGC
Sheikh Gumi ya kuma gargadi Ahlussunnah da su kauce wa fada da wadanda ke da akida ta daban, ya ce rashin biye musu yana da fa’idoji da dama.
Ya kara da cewa jayayya da tashin hankali ba za su taimaki addini ba, sai dai su kara dagula lamura.
Kiran Ahmad Gumi ga Abba Kabir Yusuf
Sheikh Gumi ya bayyana cewa gwamnati na da rawar da za ta taka wajen farfado da sahihin karatun addini a cikin al’umma.
Ya ce idan gwamnati ta dauki nauyin shirya karatun tafsirin Alkur’ani, Hadisai da Fiqhu daga malamai na gaskiya, jama’a za su gane hakikanin addini da akidar gaskiya.
Malamin ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen rage tasirin malamai masu yada koyarwar da ke kawo rudani kuma kowa zai fahimci inda aka dosa.
Bincike kan karatun Triumph a Kano
A halin yanzu, kwamitin shura na jihar Kano ya karbi korafi da aka shigar kan Sheikh Lawan Abubakar Triumph, inda ake zarginsa da kalaman batanci.
Kwamitin ya ce yana gudanar da bincike domin gano hakikanin gaskiya kafin daukar mataki na gaba.
Haka kuma, ya bukaci sauran malamai a wasu jihohi da su daina tsoma baki cikin lamarin har sai an kammala binciken cikin lumana.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun tare babbar hanya a Zamfara, sun sace shugaban majalisar Malamai
Sheikh Gumi ya yi kira ga Hamas
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan sulhun da ake kokarin yi tsakanin Hamas da Isra'ila.
Malamin ya yaba da matakin da Hamas ta dauka na yarda ta saki fursunonin Isra'ila da ta kama a shekarun baya.
A yanzu haka dai ana cigaba da caccaka tsinke a kasar Masar domin ganin an kammala samun daidaito da tsayar da yakin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

